✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutane sun gudu dazuka bayan Boko Haram ta kai hari kauyuka 3 a Borno

Boko Haram ne sun kai hari kauyuka uku da ke karamar hukumar Hawul ta jihar Borno. To

Wasu mahara da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hari a kauyuka uku da ke karamar hukumar Hawul ta Jihar Borno.

Rahotanni sun ce maharan sun shiga kauyyjab Tashan Alade, Shaffa and Khiributu inda su ka kaddamar da hare-haren.

Daruruwan mazauna yankunan ne dai suka tsere suka bar gidajensu, a daidai lokacin da ‘yan ta’addan ke ci gaba da harbi kan mai uwa da wabi.

Akasarin mazauna dai sun rika tserewa suna neman mafaka a makwabtan kauyuka da kuma dazuka.

Wata majiya daga ‘yan kato da gora a yankin ta ce maharan sun ji wa majami’un EYN biyu a kauyen Tashan Allade kawanya, lamarin da ya tilasta wa mutanen tserewa.

Kazalika, wani dan rundunar tsaro ta Civilian JTF, Balami Yusuf ya ce yanzu haka suna can suna ruwan wuta a kauyukan Shaffa da Khiributu.

“Maganar da nake maka yanzu haka suna nan suna harbe-harben, kai ma da kan ka za ka iya jiyo karar harbi.

“Mun gudu cikin dazuka, mutane kowa gudu ya ke, yara kuma sai kuka suke yi, ba mu san inda za mu sa kanmu ba,” inji Balami.

Idan za a iya tunawa, ko a jajibirin Kirsimeti sai da mayakan suka kai hari garin Garkida da ke da iyaka da Karamar Hukumar ta Hawul, inda suka kashe akalla mutum shida da kuma kone gidaje da dama.