✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane na tona gidan tururuwa don neman abinci a Borno —Ma’aikaciya

Daji suke zuwa neman abinci a gidan tururuwa, duk kuwa da matsalar rashin tsaro da macizai da ke yankunan

Mutane sun koma tona gidajen tururuwa ko za su samu abinci, saboda tsananin yunwa a wasu yankunan Jihar Borno.

Ma’aikaciyar wata kungiyar agaji da ke aiki a Jihar Borno, Fatima Muhammed Habib, ce ta bayyana haka ga BBC.

Ma’aikaciyar ta ce, “Saboda tsagwaron yunwa haka za ka ga mata na tona gidan tururuwa don samu abinci, haka mata ke ƙungiya suna yawo don neman gidan tururuwar da za su samu abinci.”

“Babban abin tashin hankalin ma shi ne daji matan ke zuwa don su samo gidan tururuwar, ga rashin tsaro a wuraren ga macizai da dai sauransu.”

Ta bayyana cewa kungiyoyin agaji suna kai wa al’ummar irin wadannan yankuna taimako, amma ba lallai ba ne taimakon ya wadace su.

Ma’aikatan kiwon lafiya da al’ummar Borno suna nuna fargaba game da karuwar yara masu fama da cutar tamowa a jihar.

Jami’an lafiya sun alakanta matsalar a jihar da rashin isasshen abinci mai gina jiki ga mata masu shayarwa.

Matsalar ta fi kamari ne a kananan hukumomi bakwai na Jihar Borno — Marte da Kukawa da Abadam da Guzamala da Kaga da Mobar da kuma Gubio.

Rahotonni sun suna cewa yara da ke kananan hukumomin sun dogara ne kacokam a kan tallafin da suke samu daga kungiyoyin agaji.

Rahoton kungiyar likitocin jinkai ta Medicins Sans Frontiers na watan Yuni inda ya nuna cewa yara 1,594 suna fama da tamowa a jihar.

Gwamnatin jihar Borno dai ta ce tana bakin kokarinta wajen kawo karshen wannan matsala.