Mayakan kungiyar ’yan ta’adda ta ISWAP sun kaddamar da wani mummunan hari a garin Rann, hedikwatar Karamar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno.
A cewar majoyoyi daga yankin, harin ya tilasta wa mazauna garin da dama guduwa zuwa makwabtan garuruwa a kasar Kamaru domin neman mafaka.
- Mutanen Jos na tururuwar zuwa kasuwanni bayan sassauta dokar hana fita
- An rataye ’yan kungiyar ISIS a Iraqi
Garin Rann dai na da iyaka da kasar Kamaru.
Rahotanni sun ce wasu gungun mayaka dauke da muggan makamai sun yi wa garin kawanya da sanyin safiyar Litinin.
Har yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, ko da yake rahotannin sun ce maharan sun kuma banka wa gidaje da dama wuta sannan suka yi musayar wuta da sojoji.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun rika kyale mutane garin na ficewa ba tare da sun yi musu komai ba.
Kazalika, shi ma wani mazaunin yankin ya ce mayakan na ISWAP daga bisani sun gudu daga garin bayan sojoji sun kawo dauki.