✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane miliyan 1 ambaliya ta shafa —Zulum

Ambaliyar ta shafe kashi daya bisa ukun Maiduguri

Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya ce mutane miliyan guda ne ambaliyar ruwa ta shafa a jihar ranar Talata.

Gwamnan ya ce ambaliyar ta shafe kashi daya bisa hudun garin Maiduguri, inda ake fargabar bullar cututtuka masu yaduwa sakamakon cikar masai da juji da sauransu.

Da yake rabon kudade da dafaffen abinci ga ’yan gudun hijirar da suka fake a Sansanin Gudun Hijira na Bukassi da ke Maiduguri, Zulum ya ce gwamnatin tarayya ta ba wa Jihar Borno tallafin Naira biliyan uku domin wadanda ambaliyar ta shafa, kuma za a yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace.

Ya ce tuni aka riga aka kafa kwamitin bayar da agajin gaggawa na lafiya domin dakile annobar ambaliyar ruwa a Maiduguri da yankin Jere.

Hakazalika, tawagar bincike da aikin ceto ta fara aiki a wuraren da abin ya shafa domin tantance irin asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi.

“Kun ga yadda ruwa ya mamaye yankin gaba daya, kazanta ta yadu, wanda hakan ne nufin za a kamu da cututtuka masu yaduwa, amma Insha Allahu za mu shawo kan lamarin.

“Zuwa yanzu dai ba mu iya tantance yawan asarar da aka yi ba, amma kusan kashi daya bisa hudu na garin Maiduguri ya cika da ruwa.

“Mutanen da abin ya shafa sun kai miliyan guda, abin da muke yi a safiyar yau shi ne ba su agajin gaggawa na abinci da sauran kayayyaki,” inji shi.

Da yake amsa tambaya kan musabbabin ambaliyar, gwamnan ya ce danganta shi da sauyin yanayi da ya haifar da mamakon ruwan sama da ake fama da shi a bana.

Ya ce ruwan ya kwace daga Madatsar Ruwan Alau, ya shigo Maiduguri, hadi yawan ruwan da aka sako daga sauran madatsar ruwa a Kamaru.

Zulum ya ba da tabbacin cewa za a sake gina madatsar ruwan tare da kara karfinta, sannan za a rushe haramtattun gine-ginen da ke kan hanyoyin ruwa da wuraren da ake fama da ambaliya.