Ƙungiyar Agaji ta Duniya wato International Committee of Red Cross ICRC, ta ce mutane 24,000 ne suka ɓace a Nijeriya, inda sama da rabin adadin yara ne.
ICRC ta fitar da alƙaluman ne yayin da ake bikin Ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin tunawa da mutanen da aka tilastawa ɓacewa saboda rashin tsaro.
ICRC ta ce an kawo mata cigiyar sama da mutane dubu 10 da su ka ɓace sanadiyyar rikicin Boko Haram a jihohin Yobe, Borno da Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Ƙungiyar ta bayyana cewa a jihohin Borno da Adamawa da Yobe, masu aikin sa-kai na ƙungiyar agaji ta Red Cross a Nijeriya sun duƙufa wajen isar da saƙonnin ƙungiyar ga iyalai da dama da mu’amala ta yanke a tsakaninsu da ‘yan uwansu saboda rikicin ‘yan bindiga.
- An sauya ranar zaɓen ƙananan hukumomin Kano
- Za mu riƙe albashin likitocin da ke yajin aiki — Gwamnati
Darektan ICRC a Afirka, Patrick Youssef ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar yayin Ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin tunawa da mutane da aka tilastawa ɓacewa, wanda aka yi a ranar 30 ga Agusta.
“Wannan rana tana ƙara wayar da kan jama’a da tunatar da su game da halin da waɗanda suka ɓace suke ciki da kuma taya ’yan uwansu alhini.
“Tare da maida hankali kan buƙatar tashi tsaye wajen ganin mutanen sun daina ɓacewa.”
Ya bayyana cewa a ya zuwa watan Yunin bana, mutum 71,000 rajistarsu ta tabbatar da cewa sun ɓace a faɗin Afirka, wanda ke nuna ƙaruwar alƙaluman da kashi 75 cikin 100 idan an kwatanta da alƙaluman da aka ɗauka a shekarar 2019.
Youssef ya yi bayanin cewa tsawaitar rikice-rikice na ‘yan bindiga, munanan bala’o’i da kuma yawan ƙaura duk sun taimaka wajen haddasa ɓacewar mutanen.
“Sakamakon hare-haren ’yan bindiga da ke ɗauke da makamai, fararen hula da mayaƙa sun ɓace.
“Suna iya ɓacewa lokacin da aka kama su ko aka tsare su. Wataƙila suna raye amma ba su da hanyar tuntuɓar danginsu,” in ji Youssef.