Akalla mutane 10,000 ne suka amfana da ayyukan kula da lafiyar kwakwalwa da walwalar jama’a na Kungiyar Agaji ta Red Cross (ICRC) a Jihar Borno.
Comfort Dauda, Jami’ar Kula da Lafiyar Ƙwaƙwalwa da Taimako ta kungiyar ICRC ce ta bayyana hakan a yayin gudanar da bukukuwan Ranar Kiwon Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta Duniya a Maiduguri.
- Abin da ya sa a yanzu Buhari yake rayuwar nadama — Solomon Dalung
- Ƙaruwar juyin mulki ya jefa Nahiyar Afirka a tsaka-mai-wuya —Masana
A cewarta, masu wannan matsala ta tabin kwakwalwa sun yi jinya a cikin shekaru takwas da suka gabata.
Ta kara da cewa, taken Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO, ta bana shi ne ‘Lafiyar hankali hakkin dan Adam ne kuma a gare mu ICRC tare da haɗin gwiwar NRCS’.
“Kungiyarmu na kula da karfafa lafiyar kwakwalwa musamman a cikin rikice-rikicen da ya dabaibaye wannan yanki a shekarun baya.”
Ta ce ICRC tana ba da tallafi na haskaka tunani ga mutanen da rikici ya shafa a jihar, tare da lura da cewa suna cikin daya daga cikin al’ummomin da za su ribaci bikin Ranar Lafiya ta Duniya.
Ta ci gaba da cewa, ICRC ta ba da tallafi na asali na zamantakewa, taimakon farko na tunani, ilimin tunani, wayar da kan jama’a, ayyukan tushen al’umma, ba da shawarar jinya kan tabin hankali da makamantan haka.
A cewarta, akwai wadanda suka amfana daga birnin Maiduguri wato Metropolitan Council sai kuma wasu a kananan hukumomin Damboa, Dikwa, Monguno da kuma Bama, inda aka basu tallafi na tsawon makonni goma na ayyukan jin kai da zamantakewa.
Ta lura cewa wadanda suka shiga ayyukan sun hada da ‘yan gudun hijira, wadanda suka bata, majinyatan asibiti da ke fama da raunukan makami, ma’aikatan kiwon lafiya, kana an yi wa mutanen da ke jinya a cibiyoyin lafiya daban-daban.
“Muna tallafa wa irin wadannan marasa lafiya a Asibitin Umaru Shehu, asibitin masu tabin hankali na jihar da asibitin kwararru na jiha da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri don samar da irin wadannan ayyuka ga wadanda abin ya shafa.
“Mun yi haɗin gwiwa da Asibitin Ƙwararrun na jiha don horar da wasu ma’aikatan jinya don tallafa wa mutanen da tashin hankali ya shafa kan tabin hankali da ayyukan tallafi na zamantakewa.
“Muna kuma aikin haɗin gwiwa tare da Ma’aikatar Lafiya da Harkokin Mata ta Jiha don ba da tallafi ga mata da ‘yan matan da aka yi wa fyade don mantawa da wannan iftila’i da ya same su ta yadda za su saki jiki don yin walwala tsakanin al’ummomin su.
“A halin yanzu muna aiki a yankuna uku a birnin Maiduguri ciki har da Ngaranam, Bayan Quarters da Libya Bayan Texaco, inda sama da mutane 340 da ke da alamomi iri ɗaya ke zuwa cibiyoyin su zauna su yi hulɗa har na tsawon makonni goma tare da ƙwararrun jami’an kula da lafiyar kwakwalwa da ƙwararrun jami’ai kan zamantakewa,” in ji ta.
Batul Bulama, wata ‘yar gudun hijira ta ce ta samu sauki daga raunin da ta samu bayan samun lafiya wadda a baya ta dan samu matsalar gushewar hankali sakamakon tallafin da ta samu daga wannan kungiya ta ICRC.
Bulama ta ce kafin a yi mata jinya a daya daga cikin cibiyoyin, ta shiga cikin damuwa kuma ta samu munanan matsalolin lafiyar kwakwalwa bayan da mayakan Boko Haram suka raba su da gidajensu.