✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙaruwar juyin mulki ya jefa Nahiyar Afirka a tsaka-mai-wuya —Masana

Mutane yanzu suna kallon sojoji a matsayin hatsabibai. Kuma lokaci ne kawai zai nuna ko da gaske ne hakan.

Da sanyin safiya ne wasu mutane sanye da kakin sojoji suka bayyana a gidan talabijin na kasar Gabon inda suka yi ikirarin kwace mulki daga hannun shugaban da iyalansa suka kwashe shekaru da dama suna mulkin kasar.

Wannan shi ne yanayi na bayan nan da ya faru a kasar Gabon a cikin watan Agusta, kuma ya zama abu sananne a wannan yanki na Afirka, yankin da ake masa lakabi da yankin “juyin mulki” inda shugabannin soja ke yin yadda suka ga dama wajen hambarar da shugabannin da jama’a suka zaba a tsarin dimokuradiyya.

Akalla dai an yi juyin mulki sau 12 a Yammaci da Tsakiyar Afirka daga shekarar 2020, inda takwas suka samu nasara yayin da sauran ko dai sun gaza ko sun fada cikin rikici.

Duk yadda lamarin yake abubuwa ne masu sarkakiya, kuma sun bambanta daga yadda kowace kasa ta kasance, amma dai masana sun yarda cewa Afirka na cikin tsaka-mai-wuya.

Shin za a kara samun dorewar mulkin dimokuradiyya a wannan nahiya ta biyu mafi girma a duniya ko kuma za ta ci gaba da fadawa hannun sojoji ne, da abin da suke fakewa suna cewa suna yin haka ne domin samar da ingantaccen shugabanci?

Juyin mulkin kasar Gabon ya faru ne sa’o’i kadan bayan da Shugaban Kasar Ali Bongo Ondimba ya sake lashe zabe a karo na uku a zaben da masu sa-ido na kasa-da-kasa suka bayyyana a mai cike da kura-kurai.

Nan take jagororin juyin mulkin suka garkame Bongo a gidan yari na tsawon mako guda.

Ali Bango ya zama Shugaban Kasar da ke Afirka ta Tsakiya mai arzikin man fetur a shekarar 2009 bayan rasuwar mahaifinsa, wanda ya mulki kasar tun 1967.

Kafin juyin mulkin na Gabon da wata guda, wasu gungun soji a Jamhuriyar Nijar sun hambarar da gwamnatin zababben Shugaban Kasar na dimokuradiyyar Mohamed Bazuom.

Kafin haka kuma, an yi juyin mulki biyu da suka samu nasara a Burkina Faso da Gini.

Sai daya a Chadi da biyu a Mali, wadanda aka yi a cikin shekara uku da suka wuce.

A cewar marubucin wani littafi a kan juyin mulki a Yammacin Afirka kuma malami a Jami’ar Janar Lansana Conte da ke Sonfaniya a birnin Konakiri na kasar Gini Mista Issaka K. Souaré, wannan shi ne karo na 100 da aka yi nasarar juyin mulki a Afirka tun bayan mulkin mallaka.

Souaré ya shaida wa kafar yada labarai ta ABC News cewa, “Hakika wannan lamari yana mayar da mafi yawan gwamnatocin kasashen baya a wannan sabon salo da aka dauka na juyin mulkin soja.

Kai hatta ga gwamnatocin sojoji da suke kan mulkin, kamar yadda ake gani a Burkina Faso.

Haka kuma zai iya sa wasu shugabanni su sake tsara fasalin tafiyar da shugabancinsu, su kuma daina tunanin yin amfani da kundin tsarin mulki don ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki, watakila wannan mataki na soja zai sa su shugabannin su yi watsi da irin wannan shiri dorewa a kan mulki.”

A mako jiya ne gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta sanar da dakile wani yunkurin juyin mulki da aka tabbatar.

A shekarar 2021 ne sojoji suka karbe mulki a Sudan, wanda tun daga wannan lokaci takaddama ta barke a tsakanin manyan bangarorin gwamnatin sojin kasar.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya soki abin da ya kira “Annoba ta juyin mulki.”

Yanzu haka ana kara nuna damuwa kan yadda yayin juyin mulkin ya bazu a kasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka.

Bamidele Olajide, malami a Fannin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Legas da ke Nijeriya, ya ce, “Juyin mulki na ta yaduwa a matsayin wani sabon yayi da yake cike da nasara, yana kuma karfafa masu son yin juyin mulki gwiwa a kasashe makwabta, musamman inda yanayin zamantakewa, tattalin arziki da siyasa suka kasance iri daya,” kamar yadda ya shaida wa kafar labarai ta ABC News.

Wannan lamari a duk tarihin yadda ya faru bai bambanta da sauran yadda aka gudanar da juyin mulki a baya ba a kowace kasa a nahiya ta Afirka.

Duk sojin da suka yi juyin mulkin suna bayar da dalilai da dama kuma kusan iri daya na hambarar da gwamnati, ciki har da cin hanci da rashawa na ’yan siyasa da kuma tabarbarewar tattalin arziki.

Sai dai mafi yawan juyin mulkin da aka yi a yankin Afirka Kudu da Sahara a bayyane yake cewar gazawar shugabannin da aka zaba na kasa magance matsalar tashe-tashen hankula da masu ikirarin jihadi a yankin Sahel na daga cikin dalilan tumbuke zababbun shugabanni daga karagar mulki tun daga shekarar 2020.

Mista Carlos Garcia-Ribero, masani mai bincike a Cibiyar Harkokin Siyasa ta Jami’ar Stellenbosch a Afrika ta Kudu, kuma farfesa a fannin siyasa a Jami’ar Valencia a kasar Spain ya ce a duk lokacin da gwamnatoci suka kasa tafiyar da lamuran kasashensu yadda al’ummar kasar ke tsammani, dole ’yan kasar su yi maraba da shigowar sojoji.

Mista Garcia-Ribero ya shaida wa ABC News cewa martanin da ’yan kasa kan bayar shi ne su fito kan tituna su yi maraba da juyin mulkin da sojoji suka yi, wanda hakan ya nuna gazawar gwamnatin da suka zaba.

An ga irin haka a bayan nan a Gabon da Nijar, inda jama’a da dama suka fito kan titunan manyan biranen kasar domin murnar juyin mulkin.

Haka masu zanga-zangar goyon bayan juyin mukin sun taru a wajen ofishin Jakadancin Faransa a Librebille babban birnin kasar Gabon da Yamai na Jamhuriyar Nijar. Kasashen Nijar da Gabon dai na da alaka ta kut-da-kut da Faransa, wadda ta yi musu mulkin mallaka a baya, kamar Burkina Faso da Mali.

Nijar kuma ta kasance babbar kawa ga Amurka da sauran kasashen Yammacin duniya wajen yaki da masu tada kayar baya a yankin Sahel.

“Wasu kasashen da suka ci gaba suna taimaka wa shugabanni wajen aiwatar da rashin gaskiya da cin hanci da kuma su ci gaba da kasancewa a kan mulki, shi ya sa juyin mulkin bayan nan ya samu goyon bayan al’umma sosai,” in ji Olajide.

Ya kara da cewa, “Mai yiwuwa ne juyin mulkin nan gaba zai fi mai da hankali kan nuna kyama ga mulkin mallaka da kuma cim ma burin kasancewa masu cikakken ’yanci kai.

“Amurka da kawayenta na bukatar ganin an samu sauya salon yin mu’amala da kasashen Afirka, saboda sojojin da suka yi juyin mulki suna cin wata moriya ta amfani da ita wajen inganta tsarin dimokuradiyya a nahiyarsu.”

A ’yan shekarun nan, gwamnatocin soja a Yammaci da Tsakiyar Afirka “Sun ci gaba da nuna bacin rai ga Faransa, kuma hakan ya sa ita uwargijiyar tasu a da, ta kasance mai nuna adawa da duk wani kokari na yin juyin mulkin da kuma fitowa ta yi Allah wadai da hakan sannan ta bayyana su a matsayin ba halattatun masu mulki ba,” in ji Olajide.

Ya ce “Mutane yanzu suna kallon sojoji a matsayin hatsabibai. Kuma lokaci ne kawai zai nuna ko da gaske ne hakan.”

Mista Souaré ya ce wani rahoto da Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP), ta fitar a bana, ya nuna cewa goyon bayan da jama’a suke nunawa ga masu juyin mulki a baya-bayan nan da aka yi a Afirka, kan iya kasancewa na wucin-gadi, kuma ba yana nufin suna kin tsarin ko rashin amincewa da dimokuradiyya ba ne, illa dai kira a samar da ingantaccen tsarin mulki na dimokuradiyyar.

“Mutane sun fito kan tituna suna murna da samun sauyi a cikin yanayi na jin dadi,” in ji rahoton na Hukumar UNDP.

A halin yanzu dai Kungiyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma (ECOWAS) da sauran kungiyoyin yankin ba su da “wani tsari na doka” da za su iya tunkarar shugabannin nahiyar da ke neman sauya kundin tsarin mulkin kasarsu domin su dawwama a kan karagar mulki.

“Wannan kuma ya sa wadannan kungiyoyi suka rasa kwarin gwiwa da amincewa a idon jama’a.

“Saboda haka, inda barazanarsu ta taimakawa wajen dakile masu son yin juyin mulki a shekarun 2000 ta yi tasiri,inda aka samu raguwar juyin mulki har zuwa shekarar 2020, lamarin a yanzu ba haka yake ba,” in ji shi.

Duk da haka, Mista GarciaRibero ya yi gargadin cewa kada a dauka kasar Gabon za ta kasance kasa ta karshe a Afirka ba da za ta iya komawa hannun soja.

“Mu sa-ido a kan Togo ko Chadi,” in ji shi. “Kuma da ni ne (Shugaban Zimbabwe Emmerson) Dambudzo Mnangagwa, da na sama wa kaina lafiaya tun da darajata,” in ji shi.