✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutane da dama sun makale bayan bene mai hawa 7 ya danne su a Kenya

Sau biyu injiniyan ginin na yin watsi da shawarar hukumomi

Rahotanni daga kasar Kenya na nuni da cewa masu aikin ceto na ci gaba da laluben gano akalla mutum 10 da suka makale a buraguzan wani benen da ya rushe a Nairobi, babban birnin kasar.

An ce galibin wadanda lamarin ya shafa leburorin da ke aiki ne a wajen gina benen mai hawa bakwai.

Iftila’in rushewar ginin ya faru ne a ranar Talata da tsakar rana a yankin Kasarani na kasar.

Rahotanni sun ce sau biyu jami’i mai sanya ido kan aikin ginin yana yin watsi da gargadin hukumomi kan a dakatar da aikin ginin duba da rashin ingancin aiki.

Har zuwa safiyar ranar Laraba, an ga tawagar masu aikin ba da agajin gaggawa na ci gaba da kokarin gano wadanda ake kyautata zaton suna nan makale a karkashin buraguzan ginin.