Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusu ya nada sabbin shugabanni a wasu hukumomin jihar guda 10 kuma nan take suka fara aiki.
Sakataren yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya ce gwamnan ya nada sabbin shugabanin ne da nufin samar da jagoranci na gari.
- ’Yan bindiga sun sace dalibai mata a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma
- ’Yan ta’adda sun kashe sojojin Nijar 60
Ga jerin wadanda aka nada:
- Salisu A. Kabo – Darakta-Janar Hukumar Tallafa wa Matasa
- Dr. Hamisu Sadi Ali — Darakta-Janar Ofishin Kula da Basuka
- Abduljabbar Mohammed Umar – Darakta-Janar Hukumar Zuba Jari (KAN-INVEST)
- Yusuf Kabir Gaya — Hukumar Ilimi a Matakin Farko (SUBEB)
- Mustapha Adamu Indabawa — Manajan Darakta Gidan Talabijin na ARTV
- Dr Kabiru Sani Magashi — Mukaddashin Shugaban Hukumar KASCO
- Aminu Aminu Mai-Famfo — Mataimaimkian Manajan Daraktan KASCO
- Hamisu Dogon Nama — Shugaban Kasuwar Kantin Kwari
- Abdulkadir B. Hussain — Shugaban Kasuwar Sabon Gari
- Abubakar Sadiq J. — Mataikain Shugaban kamfnain Kano Line.
Ya bukace sud a su yi amfani da kwarewarsu a yayin sauke nauyin da aka rataya musu, kuma da su ba wa gwamnan kunya.