✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulunci na kyamar cin zarafin kananan yara – Kabiru Sa’ad

Rahotanni daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam na nuni da cewa kananan yara suna fuskantar matsalar cin zarafi, wane mataki kungiyarku take dauka domin magance…

Rahotanni daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam na nuni da cewa kananan yara suna fuskantar matsalar cin zarafi, wane mataki kungiyarku take dauka domin magance hakan?

Cin zarafin al’umma ko yara kanana a wannan al’umma ya zama ruwan dare. Za ka ga ko’ina matsalar ke nan, ko ta fyade, shaye-shayen kwayoyi da sauran miyagun ayyuka, wanda wannan al’umma tamu ta Muhammad (saw), wadda al’umma ce ta tarbiyya, al’umma ce da ta san ya dace. Yadda ake cin zarafin kananan yara, abin mamaki ne, wanda ba haka Musulunci ya koyar ba. Ko a koyarwa ta zamantakewa, Musulunci ya nuna cewa yara mutane ne masu matukar muhimmancin gaske, masu daraja da ya kamata a rike su, a rika ba su kulawa sosai. Amma yanzu ba haka ba ne, matsalar wasu mutane ita ce suna da yara, ba su damu da cinsu da shansu ba ko kula da lafiyarsu ko suturarsu ba amma sai ka ga an yi watsi da su, an bar su. Wannan kuma ba koyarwar Musulunci ba ce, tun da Musulunci ya nuna mana kowa a gidansa shugaba ne, ’ya’yanka da Allah Ya ba ka amana ce gare ka, domin za a tambayi kowa a kan iyalansa gaba daya. Ya kamata mutum ya kiyaye.

Ko me kungiyarku take yi na kawo karshen cin zarafin yara da ake zargi ana yi, lura da cewa kowace kusurwa ta kasar nan na fama da wannan matsala?

To, idan ka kula kamar kwanan baya mun rika bin masallatai da kuma sauran unguwanni da Musulmi suke da zama, birni da kauye domin mu ga ina ne ake cin zarafin al’umma, domin mu dakile shi. Alhamdu lillahi kuma mun yi nasara kungyar mu ta tashi tsaye haikan domin hana cin zarafin yara. Mun umurci malamai a kodayaushe su rika yin wa’azi suna fadakar da mutane illar cin zarafin yara. Babbar matsalar yadda muka gano mutane yanzu wasu sai a hankali, babu cikakken ilmin addini ko tarbiyya.

Wadanne hanyoyi kake ji za a bi domin magance hakan?

To, magance wadannan matsaloli abubuwa ne masu damar gaske. Farko, sai gwamnati ta shigo saboda idan aka kafa doka ko fadakar da jama’a illar cin zarafin yara a rika hukunta duk wanda aka kama, ake zarginsa da aikata hakan gaban kotu. Sannan gwamnoni su samar wa matasa aikin yi domin magance zaman kara zube, ta ba su tallafi kadan domin su samu abin yi. Matukar babu wannan ka ga dole matsala ta zo. Da zarar matashi yanzu ya zauna babu wani aikin yi, tunaninsa zai koma namen abin da zai aikata na shaidanci. To, gaskiya sai an hada hannu, masu hannu da shuni sai sun taimaka. Su ma malamai, kamar misali, a taron da kungiyar NASFAT ta yi kwanan baya a nan Kalaba, ai ka ga an dauki yara matasa da daman gaske, an tura su koyon sana’o’i daban-daban to amma da suka gama sai aka bar su kara zube. To yaya za su yi su yi aiki da abin da suka koya? An tallafa masu an koyar da su sana’a amma babu tallafin kudi da za su sayi abin yin sana’ar, an bar su ba kudi, ba jari. Don haka sai ka ga hakan ya zama shiririta. Amma idan an tallafa musu, ka ga ko daba mutum yake yi sai ka ga ya daina.

Ko kungiyarku na da yunkurin bude wata cibiya ta koya wa matasa sana’a?

Gwamnati ce ya kamata ta yi ko ta rika baiwa matasa tallafi, musamman wadanda suke zaune babu sana’a kuma da wadanda suka gama makaranta ba su samu aikin yi ba. Ka san taimako a wannan yanayin yana da wahala, kafin a ce ga wani wanda zai fito ya ce ya yarda zai bayar.

Wata matsala da ta kunno kai shi ne yadda yara matasa ke shan miyagun kwayoyi, lamarin da har wani babban basarake a Arewa ya koka. Shin wane mataki ko hanya kungiyarku ke bi domin raba wadancan matasa da shan kayan maye?

Lamari ne babba da nake ji ban yarda ba, sai daga baya na zo na fara gani. Ai ni ji nake yi ko mutanenmu na Arewa ne kadai suke yi, amma rannan da muke dan zagaya gari muna aiki, na kama yara da daman gaske ’yan jami’a, wadanda ’yan asalin Kurosriba ne, matasa wadanda ba Musulmi ba da kwalaben wannan kayan maye; yawancinsu sun dawo daga makaranta, mazansu da matansu, sun kai su goma. Muka kirawo su, muka ce me kuke sha? Suka kasa bayar da amsa, sai muka ce bari mu kai su wajen likita ya auna su. Sai suka ce mani ai da gaske suna sha. Na tambaye su don me suke sha, sai suka ce don kwakwalwarsu ta yi sama. Sai na ga ashe ba ’yan Arewarmu kadai ba ne ke shan kayan maye. To wannan lamari ne wanda gaskiya ya kamata gwamnati ta shigo ciki.