✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulunci a tsakanin sakacin mabiyansa da mugun shirin makiya

Daga Yusuf bn Abdulwahab Abu Sunaynah Masallacin Baitul Mukaddas da ke Kudus   Fassarar Salihu Makera Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya aiko ManzonSa…

Daga Yusuf bn Abdulwahab Abu Sunaynah

Masallacin Baitul Mukaddas da ke Kudus

 

Fassarar Salihu Makera

Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya aiko ManzonSa da shiriya da addinin gaskiya domin Ya daukaka shi a kan sauran addinai koda mushirikai ba sa so. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ba Ya da abokin tarayya a suna da siffofi da uluhiyyarSa. Ya tsarkaka daga abin da masu wuce iyaka suke fadi. Sammai bakwai da kasa da abin da ke tsakaninsu suna yi maSa tasbihi game da tsarkake Shi, sai dai ku ne ba ku gane tasbihinsu. Hakika Allah Ya kasance Mai yawan hakuri Mai yawan gafara.

Kuma na shaida Annabi Muhammadu bawan Allah ne kuma ManzonSa. Manzon tsira da shiriya da aka aiko a matsayin mai bushara da gargadi ga duniya. Allah Ya shiryar da mutane ta hannunsa, kuma da shi aka rufe aiko sako da wahayi aka kammala addini. Kalmominsa suna shiryar da mu zuwa ga maganin duk wata cuta, su warkar da mu daga hassada da kiyayya a tsakaninmu. Allah Ya aiko shi da dokoki da ka’idoji, duk wanda ya bi shi tabbas zai samu nasara.

Ya Allah Ka kara tsira da aminci a gare shi da alayensa tsarkaka da sahabbansa da suka kai matuka wajen kyawawan halaye, wadanda suka tsare wannan addini daga kirkire-kirkire, suka tsare addinin har muka iske shi.

Bayan haka, hakika mafi alherin shiriya shi ita ce shiriyar Annabi Muhammad (SAW), kuma shi ne mafi kyawun abin koyi, wannan ne ya sa Allah Ya ce a cikin LittafinSa “Lallai abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasance yana fatar rahamar Allah da Ranar Lahira, kuma ya ambaci Allah da yawa.” (K:33:21).

Allah Ya karfafa batun bin Sunnar Annabi (SAW) da girmama ta, bin ta yana jagoranci ga samun kyakkyawar rayuwa da tsira da samun duk wani alheri da mutum yake fata. Muna rokon Allah Ya ba mu kyakkyawar rayuwa a duniya da Lahira.

Ya bayin Allah! Muna rayuwa a wani yanayi mai matukar wahala da radadi, yanayi ne wanda yake cike da tsanani da kunci da bala’o’i. Mu dubi yadda makiya Musulunci suka hade kansu a kanmu, ba su hada kai irin wannan, face suna kulla wa Musulunci da Musulmi makirci. Mu tambayi kawunanmu tambayoyi masu zuwa: Me ya sa suke ta cutar da mu? Shin mu ba bayin Allah mabiya ManzonSa mai girma ba ne? Idan amsar ita ce eh haka ne, to me ya sa suka hade mana baki suke kokarin share mu daga bayan kasa?

Mu waiwaya baya mu ga yadda Musulmi suke a zamanin Manzon Allah (SAW) da sahabbansa, dukan sahabbai ababen koyi ne gare mu saboda sun koyi addinin kai-tsaye daga Annabi (SAW). Sun sadaukar da komai nasu saboda wannan addini, domin tauhidi ya daukaka. Sun sadaukar da daukacin rayuwarsa saboda Allah, munafunci bai samu gurbi a zukatansu ba, ba su dauki addini wani nauyi abin damuwa ba, suna da karfin imani da yakini. Sai suka yi karfin da dan Adam bai taba ganin irinsa a tarihi ba, sun daukaka tutocin jihadi zuwa kowane sako da lungun duniya. Daga cikinsu akwai Shugaban Masu Shahada Hamza Bappan Annabi (SAW), wanda ya taba marin Abu Jahil a fuska ya yi masa rauni saboda Manzon Allah (SAW).

Wani misali shi ne na Khalid Ibn Al-Walid, wanda bayan ya Musulunta ya fafata a kowane yaki da ya gudana, kuma duk da cin kasasshe da dama, gabas da yamma, sai ga shi ya dawo ya rasu a gadon barcinsa. Wannan babban darasi ne ga duk wani matsoraci!

Abu Kattada ya ruwaito Manzon Allah (SAW) yana cewa game da sahabin nan Amr Ibn Al-Jamuh ya ce: “Zai shiga Aljanna tare da gurguwar kafarsa” Ahmad da Ibn Shaibah da sauransu suka ruwaito.

Allah Madaukaki Ya ce, “Daga muminai akwai wadansu mazaje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah alkawari a kansa: a cikinsu akwai wanda ya biya bukatarsa (wato ya yi shahada): kuma daga cikinsu akwai wanda yake jira: kuma ba su musanya ba, musanyawa.” (K:33:23).

Mahaifiyar Anas Ibn Malik ta nuna kyakkywan misali lokacin da ta ki ta auri wani Bakuraishe mai dukiya ta ce, sai ya Musulunta.

Ya bayin Allah! Wani abin da ya kamata ku yi nazarinsa a tsanake shi ne; babban hadarin da wannan al’umma take fuskanta, na yadda ake ganin yin aiki nagari a matsayin barna, sannan ake kallo barna a matsayin abu mai kyau, idan haka ya auku to, karshen wannan al’umma ya zo!

Ya taron masu Sallah! Shin mutane suna kallon kyakkyawar dabi’a abar kyama ko a’a? Ko kuwa mutane sun rude ne ba su iya bambance tsakaninsu? Caca ta watsu, ana bubbude gidajen giya barkatai, sata tana gudana a ko’ina, hatta a cikin Masallacin Al-Aksa (da sauran masallatai). Za ku ga hatta a watan Ramadan muna fama da barayi a masallatai, ana sata ga maza da mata da suke zuwa masallatan don yin Sallah. Almudahana da cin hanci da rashawa sun watsu hatta a kan tituna, matasanmu sun koma ’yan kwasar ganima da neman tara abin duniya ta kowane hali ba tare da ana sanya ido kansu ba!

Idan wani ya rasa dukiyarsa zai nemi mayar da ita, idan suka rasa lafiya sukan nemi magani nan da nan, amma idan wani ya rasa imani, sai ya zamo kamar ya mutu! Ya bayin Allah! Mene ne dalilin faruwar wadannan abubuwa? Wace hanya ce ta fi dacewa don fita daga wannan jarrabawa da mummunan hali?

Amsa daya ce, kuma a fili take; duk mun san ta, wato komawa ga Allah. Allah Ya ce: “Lallai wannan Alkur’ani yana shiryarwa zuwa ga (halaye) wadanda suke mafi daidaita, kuma yana bayar da bushara ga muminai wadanda suke aikata ayyuka na kwarai (cewa) suna da wata ijara mai girma.” (K:17:9). Kuma Ya ce, “Kuma lallai wannan ne tafarkiNa, yana madaidaici: sai ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyi, su rarrabu da ku daga hanyaTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi, tsammaninku kuna yin takawa.” (K:6:153).

Kuma Ya ce, “Ka ce, “wannan ce hanyata; ina kira zuwa ga Allah a kan basira, ni da wadanda suka bi ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Ni kuma, ban zama daga masu shirki ba.” (K:12:108).

Ina tambayarku gaba daya: Wane ne daga cikinku yake bin wannan umarni daga Allah? Wane ne ya yi imani da Allah, imani na gaskiya? Wane ne zai yi jihadi a tafarkin Allah kuma ya yi aiki don jin dadin Musulmi da Musulunci? Wane ne a cikinku yake da kyakkyawar niyyar yin komai saboda Allah kadai?

Ya ku muminai! Ma’aiki (SAW) ya aiki babban sahabin nan Mus’ab Ibn Umair zuwa Madina don ya ilimantar da makiya Musulunci (a wancan lokaci). Mus’ab ya tafi don isar da sakon Allah, Alkur’ani ne makaminsa. Wannan yana nuna shiriya ta gaskiya ita ce shiriyar Allah; ita ce hanya madaidaciya, kuma ita ce cikakkakiyar wayewa. Mus’ab ya kai Musulunci kowane gida a Madina, ya kai shiriya kowane gida, yana dauke da Alkur’ani kawai, kuma Alkur’ani ya fi kowane makami amfani.

’Yan uwa a Musulunci! Mutum guda kadai ya yada Musulunci a daukacin birnin Madina; mutumin da bai damu da kawar duniya mai karewa ba. Kuma Ma’aiki (SAW) ya ba shi tutar yaki a ranar Yakin Uhudu, ya tafi fagen daga sanye da tsohuwar riga mai face-face- amma sai ga shi ya wayi gari cikin ’yan Aljanna. Kafin ya Musulunta yakan sanya suturar siliki, ya fi kowa caba ado a Makka, amma sai ga shi ya dauki tutar Musulunci sanye da raggan kaya. Ya yi jihadi sosai a fagen daga, ba tsoro ko kasala, bai juya baya ga makiya ba, kai a sahun gaba yake a koyaushe yana fafatawa da makiya. Sai aka sare hannunsa na dama, sai ya mayar da tutar hannun hagu har sai da aka sare daya hannun. Sai ya rike tutar tsakanin dungulmin hannuwansa, sai da takobin makiya ya raba shi da ransa ya koma ga Allah!