Al’ummar Rohingya da ke gudun hijira a Birtaniya da Amurka sun gurfanar da Kamfanin Facebook a gaban shari’a kan zargin iza wutar rikici a shafukan sada zumunta ta hanyar barin kalaman kiyayya a kansu, kamar yadda Sashin Hausa na BBC ya ruwaito.
Sun bukaci Facebook ya biya su diyyar Dala biliyan 150 kan ikirarin da ya rawa wajen rura rikicin da ya kai aka kashe daruruwan Musulman Rohingya.
- ’Yan IPOB sun kashe ’yan Arewa sama da mutum 137 – Bincike
- Mahaukaciyar guguwa ta hallaka sama da mutum 100 a Amurka
An yi kiyasin cewa an kashe Musulman Rohingya 10,000 lokacin da sojoji suka kaddamar da hare-hare a yankunan da mabiya addinin Buddha suka fi rinjaye a Myanmar a shekarar 2017.
Kawo yanzu Kamfanin Facebook, wanda ya koma Meta, bai mayar da martani kan zargezargen ba.
Zargin ya biyo bayan wallafa kalaman kiyayya da batanci masu hadarin gaske da aka yi ta yadawa shekara da shekaru.
Kungiyar lauyoyi a Birtaniya da ke wakiltar ‘yan gudun hijirar ta rubuta wasika ga Facebook.
A Amurka lauyoyi sun shigar da korafi kan Facebook a San Francisco kan zargin “sanya rayuwar ’yan Rohingya cikin hadari, domin biyan bukatar kai da samun kasuwa a ‘yar karamar kasar da ke kudu maso yammacin Asiya.
Sun bayar da misali kan wani sako da aka wallafa a shafin Facebook da Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa, ciki har da wanda aka yi a shekarar 2013 da ke cewa: “Mu yake su kamar yadda Hilter ya yaki Yahudawa.”
Wani kuma na cewa: “Ku zuba musu fetur, sannan ku banka musu wuta, ta haka za su fi saurin isa ga Ubangiji.”
Facebook yana da sama da mabiya miliyan 20 a Myanmar. Ga yawancinsu shafukan sada zumunta su ne kadai hanyar da za su yada labarai.
A shekarar 2018, Facebook ya amince cewa bai dauki matakan da suka kamata ba wajen kare kalaman kiyayya da tuzuri a kan ’yan Rohingya. Wannan ya biyo bayan wani rahoto da ba na gwamnati ba da Facebook ya gabatar da ke cewa shafin ya bayar da damar yin cin zarafin dan Adam da iza wutar rikicin. K
ura-kuran baya da Facebook ya yi na farautarsa Abin da ya faru a Myanmar shi ne abu na farko da ya fara shafa wa Facebook kashin-kaji. Shafin sada zumuntar yana da matukar farin jini a yankin, amma Kamfanin bai fahimci ainihin abin da ke faruwa a shafin ba.
Ba su sake duba bayanan da aka wallafa da harshen mutanen Burma da Rakhine ke amfani da su. Da sun bincika, da kuwa sun ga yadda ake ta wallafa kalaman kiyayya ga Musulmi da labaran karya da ake yadawa akan hareharen da ‘yan ta’addar Rohingya suka kai. Masu sukar lamiri sun ce wannan ya taimaka wajen iza wutar rikicin da ta kai ga mummunan tashin hankalin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban rayuka.
Mark Zuckerberg da kan sa ya amince da cewa sun tafka kuskure a kan karuwar rikicin a Myammar.
Wannan ne ya sa ainihin karar da aka maka facebook ta zama mai daukar hankali kuma Kamfanin bai musanta gazawarsa ba.
Ko ma yaya lamarin yake, a shari’ance sun taka rawa kan mummunan abin da ya faru da sanya rayuwar ’yan Rohingya cikin hadari.
Abin tambayar shi ne ko tafiyar za ta yi nisa kan shari’ar? Watakila ta yi, watakila kuma ta bi shanun-sarki.
Sai dai Meta na kokarin kawar da hankali daga Facebook saboda har yanzu kura-kuran da ya tafka a baya na ci gaba da farautarsa.
Ana kallon ‘yan Rohingya a matsayin ‘yan gudun hijirar da suka je Myanmar ba bisa ka’ida ba, kuma shekaru da dama gwamnati da kanta ta nuna musu wariya.
A shekarar 2017, sojojin Myanmar suka kaddamar da hare-haren kakkabe ’yan Rohingya daga Jihar Rakhine bayan wani mummunan hari da masu dauke da makamai a yankin sun kai wa ‘yan sanda.
Dubban mutane ne suka mutu, yayin da wasu 700,000 suka tsere daga kasar zuwa makociyarta Bangladesh.
Akwai kuma zarge-zargen da aka yi ta yadawa kan cin zarafin dan Adam, ciki har da kisan gilla da fyade da kona gidaje da gonaki da ake yi wa sojojin Myanmar.
Har wa yau, a shekarar 2018, Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Facebook da tafiyar hawainiya wajen daukar matakin gaggawa kan bayanan da ake yadawa a shafin.
Karkashin dokokin Amurka, Facebook na da babbar kariya kan daukar alhakin abin da masu amfani da shafin suka wallafa.
Sai dai lauyoyin da suka shigar da sabon korafin sun ce babu wannan tanadin karkashin dokokin shari’a na Myanmar, don haka da su za a yi amfani da wajen sauraren karar (BBC).