Wasu Musulmai mabiya mazhabar Shi’a a ranar Lahadi sun ziyarci wata majami’a da ke Zariya a Jihar Kaduna don taya su murnar Kirsimeti, sannan suka ba su kyaututtuka.
Sun kai ziyarar ce yayin ibada a majami’ar Ekelisiyar ’Yan Uwa ta Nigeria (EYN) da ke Samaru a Zariya, a matsayin wani bangare na nuna kaunar juna da inganta zamantakewa tsakanin mabiya addinai daban-daban.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Kyauta A Addinin Kirista
- Jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda 100 a rana guda a Borno
Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala ibada a majami’ar, jagoran tawagar, Farfesa Isa Mshelgaru, ya ce makasudin kai ziyarar shi ne taya Kiristoci murnar ranar haihuwar Yesu Almasihu.
Ya kuma ce, “Musulunci ya ce idan wani bai zama dan uwanka na addini ba, zai zama dan uwanka na mutuntaka. Kuma da mu da su duk mutane ne, duk da addinanmu sun bambanta.
“Mun yanke shawarar kai wannan ziyarar ce ga wannan Cocin saboda yau ce ranar Kirsimeti, ranar da aka haifi Yesu Almasihu, wacce ake bikinta a duk fadin duniya, shi ya sa muka zo mu nuna musu kauna.”
Farfesa Isa ya kuma ce Musulmai na daukar Kiristoci a matsayin ’yan uwansu na mutuntaka, inda ya ce irin wannan alakar na da matukar muhimmanci, musamman la’akari da yanayin da Najeriya take ciki a halin yanzu.
Ya kuma ce ya zama wajibi dukkan ’yan Najeriya su hada karfi da karfe ba tare da la’akari da banbance-banbacen addini ko kabila ko kuma na siyasa, wajen ceto kasar.
Shi ma a nasa jawabin, Faston Cocin, Rabaran Tijjani Chindo, ya ce sun karbin bakin nasu cikin farin ciki, sannan ya yi kira da a yi irin haka a fadin Najeriya.
Rabaran Tijjani ya kuma shawarci ’yan Najeriya da su koma ga Allah tare da neman zabinSa a daidai lokacin da babban zaben 2023 ke dada karatowa.