✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulmai na karuwa a Birtaniya da Wales

Yawan Musulmai kuma ya kai miliyan 3.9 ko kuma kashi 6.5 cikin 100.

Kididdigar yawan al’ummar Birtaniya da Wales ta nuna cewa, adadin Musulmi na karuwa, yayin da adadin Kiristoci ya gaza rabin jama’ar yankunan biyu, kuma a karon farko ke nan da ake samun haka.

Kididdigar wadda aka saba fitar da ita duk bayan shekaru 10, ta nuna yadda yawan Musulmai ke habaka, amma dai babu addinin da ke da mabiya masu tarin yawa kamar Kiristanci.

Mutane miliyan 27.5 ko kuma kashi 46.2 cikin 100 sun gabatar da kansu a matsayin Kiristoci a Ingila da Wales a kididdigar ta 2021, lamarin da ke nuna cewa, adadinsu ya ragu da kashi 13.1, idan aka kwatanta da kididdigar shekarar 2011.

Yawan Musulmai kuma ya kai miliyan 3.9 ko kuma kashi 6.5 cikin 100, lamarin da ke nuna cewa, adadin Musulman ya karu daga kashi 4.9 a kididdigar 2011.

Mabiya addinin Hindu ne ke matsayi na uku wajen yawan mabiya a Birtaniya da Wales, inda suke da yawan da ya kai miliyan 1.