Shugaban Kasar Uganda, Yoweri Museveni ya sake lashe zaben shugaban kasar a karo na shida bayan da ya sami nasara da kaso 56 cikin 100 na kuri’un da aka kada.
Hukumar zaben kasar ce dai ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben ranar Asabar, bayan ya doke babban abokin hamayyarsa daga cikin ragowar ’yan takarar su 10, Boby Wine wanda ya sami kaso 34.4 cikin 100.
Shugaban Hukumar Zaben Kasar, Mai Shari’a Simon Mugenyi Byabakama ya ce, “Hukumarmu ta ayyana Yoweri Museveni a matsayin sabon zababben Shugaban Jamahuriyar Uganda.”
Ya kuma ce an sami kimanin kaso 57.22 cikin 100 na masu kada kuri’a miliyan 18 a kasar da suka fito zaben, yana mai kira ga ’yan kasar da su kwantar da hankulansu kuma su karbi sakamakon da zuciya daya.
To sai dai babban abokin hamayyar Shugaba Museveni, mai kimanin shekaru 38, Boby Wine ya ce zaben cike yake da almundahana da magudi.
Jam’iyyar Boby ta NUP ta dage cewa an yi wa dan takarar nata wanda a da mawaki ne daurin talala a gida, ko da yake gwamnatin kasar ta ce ta yi hakan ne domin samar masa da cikakkiyar kariya.
A yanzu dai shugaba Museveni ne shugaba mafi dadewa a a kan mulki a nahiyar Afirka inda ya shafe shekaru 35 a kan mulki.