✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Safina Namukwaya: Mai shekara 70 ta haifi tagwaye a Uganda

Maza ba sa son jin kina dauke da cikin tagwaye, tun lokacin da aka kawo ni a nan mijina bai taba zuwa ba.

Wata dattijuwa ’yar kasar Uganda ta kafa tarihin zama mace mafi tsufa da ta haihu a nahiyyar Afirka.

Matar mai suna Safina Namukwaya mai shekaru 70 ta haifi tagwaye ne bayan da ta samu juna biyu ta hanyar ƙyanƙyashe ƙwai a dakin bincike kafin a dasawa mace a mahaifa (IVF).

Cibiyar kula da lafiyar mata ta ƙasashen duniya da cibiyar haihuwa da ke Kampala babban birnin Uganda, ta ce Safina ta haifi namiji da mace.

“Wannan ba abu ne kaɗai ya yake nuna ci gaba a fanni likitanci ba amma harda nuna jajircewa na ɗan Adam,” in ji asibitin a shafin Facebook, biyo bayan nasarar haihuwa da Namukwaya ta yi ta tiyata a ranar Laraba.

Safina Namukwaya ta shaida wa gidan talabijin na NTV mai zaman kanta cewa wannan ne karo na biyu da ta haihu cikin shekaru uku, bayan ta haifi yarinya a shekarar 2020.

Ta kara da cewa ta fuskanci matsaloli da dama a lokacin da take dauke da juna biyu, ciki har da rabuwa da mahaifin yaran.

“Maza ba sa son jin kina dauke da cikin tagwaye, tun lokacin da aka kawo ni a nan mijina bai taba zuwa ba.”

Namukwaya ta ce ba ta san yadda za ta yi renon yaran ba, amma ta yi farin ciki da samun su bayan shekaru da dama da suka sha fama na rashin haihuwa.