✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Musanta juna biyu: Ina hikimar A’isha Buhari?

A ra’ayina bai kamata Hajiya Aisha ta kula labarin ta samu juna biyu ba.

Bisa ga halayya da dabi’ar dan Adam, mata sun fi maza buri da fatan su haihu kuma ana gane haka daga irin yadda duk lokacin da wata jarida ko mujalla ta yi hira da wata mace a kan rayuwarta.

Galibi idan aka tambaye ta abin da ya fi faranta mata rai, muddin ta yi aure kuma ta haihu, za ka ji ta ba da amsa da cewa lokacin da ta samu juna biyu, ta sauka lafiya ta kuma ga abin da ta haifa.

Wadansu ma sukan kara da cewa ganin yaranta suna kai-kawo gabanta, ko su ma sun zama masu gidanjen kansu da ’ya’ya, wato jikokinta.

Yawaitar karanta irin haka da nake yi, ya sa wata rana na tambayi wata mata ko me ya sa haka? Sai ta ce da ni.

Ka san mata suke da halittar su haihu, don haka su ake yi wa gorin ba sa haihuwa.

Ba kasafai za ka ji ana yi wa namiji gorin ba ya haihuwa ba, amma mace da zarar ta yi aure ba ta haihu ba, za ta yi ta fama da gori da tsangwama, musamman daga ’yan uwan mijinta, a kan cikin cin tuwo take da shi, bare ma a ce mijin ya taba haihuwa.

Mai karatu yau da gobe, ta sa a kullum ina kara fahimtar amsar waccan mata.

Kafin zuwa wannan lokaci da Yahudawa da Nasara da ire-irensu, suka cusa mana kamfen din takaita haihuwa.

A baya can kakanninmu da iyayenmu da yayyenmu mata sun yi ta haihuwa, mace daya ta haifi ’ya’ya 12 zuwa sama, kuma ka gan ta dakar.

Sabanin maza da matan wannan zamani da wasunsu sun fara haihuwa, sai su fara shiga shirin kayyade iyali.

Ko irin wadancan ma’aurata kan manta cewa haihuwa kyauta ce daga Allah kuma ba mai ba da ita sai Shi ga wanda Ya so a lokacin da Ya so?

Mai karatu wannan ’yar shimfidar da na yi ita za ta kai mu ga mukalar wannan mako, dangane da labarin da yayar wannan jarida Daily Trust ta ranar Laraba 22 ga Disamban nan ta buga a shafinta na 6, mai kanun: “AISHA BUHARI TA ‘MUSANTA’ TANA DA JUNA BIYU, TA KUMA TURA MA’AIKATANTA ZUWA HUTUN SAI ILLA MASHA ALLAHU.”

Musantawar da hadimanta biyu Malam Sulaiman Haruna da Malam Mohammed Kamal Senior suka yi ta kafofi daban-daban kuma a lokuta daban-daban, ba ta rasa nasaba da yadda kafofin yada labarai na zamani suke cike da labari a makon jiya, bayan Aisha Buhari ta dawo daga kasar Turkiyya tare da mijinta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Malam Sulaiman ya fada wa sashin Ingilishi na BBC, cewa Aisha Buhari ba ta dauke da juna biyu, kuma tana nan lafiya kalau.

Ya kara da cewa labaran da ake yadawa jita-jita ce kuma daga wadanda ba su fatan alheri.

Kai ka ji mai karatu samun juna biyu ga matar aure shi ne ba a yi mata fatan alheri. Ko sai me zai same ta a yi ma ta fatan alheri, da ya fi samun karuwa irin ta mutum?

Shi kuwa Malam Kamal Senior sanarwa ya bayar inda ya ce, Uwargidan Shugaban Kasar ta umarci dukkan ma’aikatanta su tafi hutun sai illa masha Allahu, yana mai cewa daga wannan lokaci duk wani abu da za ta yi, za ta rika gudanar da shi ta hanyoyin na’urar zamani, kamar yadda ta rika yi a baya.

Tarihi ya tabbatar da cewa, tun a ranar 2 ga Disamban 1989, aka daura auren Hajiya Aisha da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda zuwa yanzu sun samu shekara 32 da wasu kwanaki.

Allah kuma Ya albarkaci auren da ’ya’ya biyar, namiji daya da mata hudu.

Da dadi ba dadi, ana nan tare, duk da irin hayagagar da Hajiya Aisha ta rika yi wa maigidanta, musamman a wa’adinsa na farko, lokacin da har ta fito karara ta fada wa duniya cewa, ba za ta yi masa kamfen ba a yakin neman zabensa don neman zangon mulki na biyu in bai yi wasu abubuwa ba.

Duk abin da ta yi yau ya zama tarihi. Kaina ya daure na kuma kidime, don na rasa hikimar musanta wancan labari na juna biyu.

Ina jin matar da ba ta da aure kuma take da babban matsayi a idon duniya, ai ita ya kamata in an zarge ta da yin ciki, za ta sa a musanta, don kauce wa abin kunya.

Ita a wane dalili? Ko tana jin don tana ’yar shekara 50 Allah ba zai iya ba ta rabo ba?

Kada Uwargidan Shugaban Kasa ta manta cewa gabaninsu, marigayiya Hajiya Maryam Babangida (Allah Ya gafarta mata), suna kan karagar mulki ta haifi ’ya mace da aka sa mata suna Halima.

Hajiya Maryam Abacha Uwargidan marigayi Shugaban Kasa Janar Sani Abacha (Allah Ya gafarta masa), a 1994, ta haifi namiji da aka sa masa suna Al-Mustapha.

Da wannan tarihi, ka ga ke nan in ma Hajiya A’isha ta haihu suna mulki ba kanta farau ba.

A sanin da na yi wa su mata idan mazansu na kan karagar mulki, na siyasa kowane iri ko na sarauta, ko yana tashen dukiya, sukan so su haihu, ko don tarihi ko don a yi masu hidimar da ba a taba yi masu ba.

A ra’ayina bai kamata Hajiya Aisha ta kula labarin ta samu juna biyu ba.

A nan ina ga kila ta ki daukar shawarar mataimakanta da suke kula da hulda da jama’a, wadanda ya kamata ta tattauna da su a kan duk sanarwar da za ta bayar, in ko ta yi, to sun ba ta gurguwar shawara, kasancewar irin wadannan labarai musanta su ba ya da wani amfani, sai ma su kara jefa mutum cikin wani ce-ce-ku-cen, kamar yadda na gani har na yi wannan rubutu.

Saura me? Allah Ya rayar da mu, mu gani kuma mu ji wa ke da gaskiya, manema labarai ko Aisha Buhari?

%d bloggers like this: