Kungiyar nan mai fafutukar kare hakkokin Musulmai a Najeriya (MURIC) ta yi watsi da sabon jadawalin da Hukumar Shirya Jarrabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta fitar na jarrabawar bana.
A wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta, Farfesa Ishaq Akintola, MURIC ta yi zargin cewa yadda hukumar ta saka jarrabawar wasu darussan a daidai lokacin sallar Juma’a abin Allah-wadai ne.
“Da gangan WAEC ta tsara jadawalin a haka saboda ta saka shinge tsakanin matasa Musulmai da kuma masallatan Juma’a”, in ji MURIC.
WAEC: Najeriya ta fidda ka’idojin jarabawa
Za a bude makarantu bayan hutun Sallah
Dakatar da WAEC a Bana: Dalibai da iyaye sun bara
“Idan aka yi duba na tsanaki a jadawalin da WAEC ta fitar kwanan nan, za a fahimci cewa akwai akalla darussa uku da aka saka a daidai lokacin sallar Juma’a a ranakun 14 da 21 ga watan Agusta sai kuma hudu ga watan Satumba.
“Wannan jadawalin neman tsokana ne, yunkurin tayar da zaune tsaye ne, neman raba kan jama’a ne da kuma rashin la’akari da Musulmai. An shirya hakan ne da gangan domin a muzgunawa Musulman da za su zana jarrabawar kuma yunkuri ne na marasa son zaman lafiya na makiya Musulunci.
“Hakan na nunawa karara cewa ba a shirya yi wa Musalmai adalci ba.
“Wannan abin takaici ne matuka bisa la’akari da cewa sai da kungiyarmu ta yi kan-da-garki ta hanyar jawo hankalin WAEC tun da farko cikin wata sanarwa a ranar Talata, 23 ga watan Yunin 2020 muna bukatar hukumar ta yi la’akari da sallar wajen shirya jadawalin amma ta yi kunnen-uwar-shegu da mu duk kuwa da cewa kiran ya baza gari a kafofi da dama”, in ji sanarwar.
MURIC ta yi kira ga hukumar ta WAEC da ta gaggauta janye jadawalin ta musanya shi da sabo wanda zai yi la’akari da Musulmai da kuma ba su damar yin ibadarsu ba tare da wani tarnaki ba.
Idan dai za a iya tunawa WAEC ta dage jarrabawar da aka saba gudanarwa a watannin Afrilu da Mayu ne saboda annobar COVID-19 da ta tilasta rufe makarantu.