Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), ya bayyana cewa Matatar Dangote da sauran matatu na gida suna da ’yancin sayar wa ’yan kasuwa kayayyakinsu kai-tsaye.
Kamfanin watsi da zargin da ake masa na cewa yana ƙoƙarin zama wanda zai ke sayan man fetur daga matatar shi kaɗai.
- Gano gawarwakin Isra’ilawa 6 da aka yi garkuwa da su a Gaza ya tayar da ƙura
- Mai magana da yawun Tinubu, Ajuri Ngelale ya ajiye aiki
NNPCL, ya mayar da martani ne kan zargin da ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi (MURIC), ta yi na cewa kamfanin ya ƙara farashin man fetur don hana matatar Dangote rage farashin man fetur a ƙasar nan.
MURIC, ta bakin Daraktanta, Farfesa Ishaq Akintola, ta bayar da shawarar cewa a bar Dangote ya gudanar da kasuwancinsa ba tare da katsa-landan ba.
Sai dai mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye, ya caccaki MURIC, inda bayyana zargin nasu a matsayin kuskure, kuma ya ce hakan zai iya hura wutar ƙiyayya tsakanin talakawa da NNPCL.
Soneye, ya bayyana cewa farashin man fetur a duniya ne ke yin tasiri a kasuwar cikin gida, ba NNPCL ba.
Ya ƙara da cewa masana’antu kamar Dangote za su iya sayar da kayayyakinsu a farashi mai rahuda idan suna so.
Ya kuma fayyace cewar NNPCL ba shi da niyyar zama wanda zai ke sayan kayayyakin Dangote shi kaɗai.