✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

MURIC ta bukaci a dage jarabawar NECO ta ranar Babbar Sallah

Kungiyar ta bukaci a dage jarabawar zuwa wata ranar ta daban

Kungiyar nan mai rajin kare muradun Musulmai a Najeriya ta MURIC ta bukaci Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta dage jarabawar da dalibai za su zana ranar Asabar, tara ga watan Yuli, saboda ita ce ranar Babbar Sallah ta bana.

Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bukaci hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi.

“Muna sane da cewa cin karon da aka samu ba da gangan ba ne, saboda NECO ta nuna sanin ya-kamata, ta hanyar ware mako guda domin bukukuwan Sallar (tun daga Litinin, 11 zuwa Juma’a 15 ga watan Yuli) kuma a jadawalinta ma ta nuna hakan.

“Saboda haka, muna kira kira da hukumar da ta sake matsar da jarabawar ranar Asabar, tara ga watan Yuli zuwa wata ranar ta daban.

“Yin hakan zai ba dalibai Musulmai damar yin bukukuwan Sallah da rubuta jarabawar.

“Darasin da aka tsara rubutawa ranar Sallar za a iya mayar da shi zuwa ranar Alhamis, 14 ga watan Yulin 2022, wacce daya daga cikin ranakun da aka saka ce domin hutun Sallar,” inji MURIC.

A makon da ya gabata ne dalibai masu shirin kammala sakandare suka fara rubuta jarabawar ta NECO wato SSCE a duk fadin Najeriya.

A bana dai, Musulmi a Najeriya kamar sauran takwarorinsu na kasashen duniya za su gudanar da bikin Babbar Sallah ne ranar Asabar, tara ga watan na Yulin 2022.

%d bloggers like this: