Kungiyar nan Mai Fafutukar Kare Hakkin Musulmai ta Najeriya (MURIC) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta biya manoma diyya wadanda Fulani makiyaya suka yi wa ta’adi a gonakinsu.
Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayayana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
- Kai wa Fulani hari ba zai haifar wa da Najeriya da mai ido ba – Bashir Tofa
- Dan Buharin Daji zai ajiye makamansa a Zamfara
A cewar kungiyar, akwai tarin hujjoji na bidiyo dake nuna yadda makiyayan suka yi wa gonakin manoman ta’adi.
Ya ce, “MURIC yanzu haka ta tura wakilanta jihohi domin tattara bayanai kan irin barnar da makiyaya suka yi a gonakin manoma.
“Mun neme su da su tattaro bayanai daga dukkan jihohin har da Babban Birnin Tarayya Abuja.
“A zahirin gaskiya kuma mun gamsu da irin bayanan da suke ba mu,’’ inji Daraktan na MURIC.
Farfesa Ishaq ya kuma yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su dauki nauyin biyan diyyar, yana mai cewa bayyane yake a zahiri cewa har yanzu Gwamnatin Tarayya ba ta fara biyan manoman diyyar asarar da suka yi ba.
“Saboda haka muna sake jaddada kiranmu ga gwamnati kan ta bullo da sabbin hanyoyin biyan diyya, muna da hujjoji da bayanai na irin barnar da aka yi.
“Hakan ne kadai zai tabbatar da wanzuwar adalci da daidaito,’’ inji shi.