Ƙungiyoyin Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) da Ƙungiyar Mata Musulmi ta Nijeriya (FOMWAN) a Jihar Oyo sun yi tir da Allah wadai da wani limamin Kirista a garin Iseyin ya ɗauka na gayyatar sojoji sama da 10.
Inda suka lakaɗa wa wani malamin addinin Musulunci da matansa biyu duka, kan sun yanka dabbobin Layya a ƙofar gidansu da ke kallon cocinsa.
- Haɗarin tirela ya kashe mutum 14 a Kano
- Lakwaja: Birnin da manyan kogunan Nijeriya suka haɗu amma ba ruwan sha
Malamin mai suna Alfa AbdulAzeez Sulaimon da matansa biyu da wasu Musulmi sun samu munanan raunuka a sassan jikinsu a dalilin dukan da sojojin suka yi masu.
Lamarin ya auku ne a Unguwar Oke-Imuse a kusa da barikin sojoji da ke garin Iseyin a inda limamin Cocin Christ Apostolic, Fasto Sunday Ogundairo ya umarci ɗaya daga cikin ’ya’yansa da yake aikin soja
mai suna Damilola ya ɗauko takwarorinsa sojoji inda suka je suka aikata wannan ɗanyen aiki a ranar Lahadi da aka gudanar da Babbar Sallar bana.
Bincike ya nuna cewa Fasto Stephen ya yanke shawarar ɗaukar wannan mataki ne domin nuna rashin amincewa ga yanka dabbar Layya ana fuskantar cocinsa da Alfa Abdul Azeez ya yi a ranar.
Shugaban Ƙungiyar MURIC reshen Jihar Oyo Ambasada Ibrahim Agunbiade ya yi kira ga mahukunta a jihar su tabbatar da cewa an kama duk wanda ke da hannu a aikata wannan ɗanyen aiki domin hukunta shi.
Ita ma Shugabar Ƙungiyar Mata Musulmi ta FOMWAN reshen Jihar Oyo, Dokta Lateefah Dairo ta nuna matuƙar baƙin ciki kan aukuwar wannan lamari, inda ta ce ɗaya daga cikin matan malamin tana ɗauke da junabiyu a lokacin da sojojin suka yi masu dirar mikiya a ƙofar
gidansu suka kama dukansu da jansu a ƙasa saboda sun yanka dabbar Layya suna kallon ginin cocinsu.
Cikin sanarwar daƙungiyoyin biyu suka aika wa kafofin Labarai a Ibadan, sun nemi gwamnatin jihar da rundunar ’yan sandan jihar su yi duk abin da ya wajaba cikin ƙanƙanen lokaci don gano dukkan masu hannu a wannan lamari domin hukunta su.
Shugaban Ƙungiyar MURIC, Malam Ibrahim Agunbiade ya nuna taƙaicin ganin faifan bidiyon da aka sa a kafofin sada zumunta da ke nuna yadda sojojin suke wulaƙanta iyalan da cin mutuncinsu ba gaira ba dalili. Ya yi gargaɗin cewa wannan ba ƙaramar magana ce da za a jefa a kwandon shara ba.
Ya ce wajibi ne ’yan sandan su zaƙulo kuma su kama masu hannu a lamarin domin a hukunta su.
Ita kuwa Shugabar FOMWAN cewa tayi limamin cocin ya yi amfani da kasancewar ɗan sa soja ne ya aikata wannan ɗanyen aiki don nuna hushinsa ga Musulmi mazauna unguwar da kwanakin baya suka kai ƙararsa ga Aseyin na Iseyin a kan damunsu da ƙarar lasifika da ke fitowa daga cocinsa.
Dokta Lateefah ta yi kira ga malamai da shugabannin addinai su tabbatar da cewa mabiynsua suna girmama juna domin zama lafiya da kwanciyar hankali.
Ta nuna taƙaici kan yadda wasu kafofin Labarai suka ƙi bayyana labarin gaskiya kan lamarin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo, Adewale Osifeso ya ce rundunar ta fara bincike domin gano daliin aukuwar lamarin.
Bayanai sun ce tuni Ƙungiyar Kiristoci (CAN) a yankin ta umarci faston ya nemi wani waje ya mayar da cocinsa can don kada ya haifar da rikicin da zai jawo zubar da jini ko asarar dukiya.