Munanan hare-hare da kishiyoyi masu mugun kishi da mugunta ke kai wa ’ya’yan kishiyoyinsu ya dauki wani salo mai firgitarwa a baya-bayan nan musamman a nan Arewacin Najeriya, inda aure mace fiye da daya ya mamaye ko’ina. Galibi kananan yaran da aka rabu da iyayensu mata sukan hadu da haka, inda suke fama da rayuwar kunci da musgunawa da aikin wahalarwa daga kihsiyoyin iyayensu da suke huce fushi da zafin kishi a kan yaran da babu mai taimaka musu.
A farkon wannan mako ne aka ruwaito wata amarya mai shekara 17 da ake zargi da yanke azzakarin wani dan kishiyarta mai kwana 23 a kauyen Dafe da ke karamar Hukumar Shiroro a Jihar neja. Ana zargin Bara’atu Muhammad da yanke azzakarin jariri Buhari Muhammad ne saboda kishi. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja DSP Bala Elkana ya ce an kama wacce ake zargin kuma an gurfanar da ita a gaban Kotun Majistare ta daya da ke Minna inda daga can aka kai ta kurkukun Minna domin zaman jiran shari’a.
Elkana ya ce Bara’atu ta yi ikirarin cewa ta yi amfani da wuka ce wajen yin wannan mugun aiki a cikin ban-dakinsu bayan ta dauke jaririn lokacin da yake kwance aa kan shimfida a cikin gidan.
Dokta Ibrahim Abdullahi na Asibitin kwararru na IBB da ke Minna, ya ce an guntule azzakarin jaririn ta yadda ba za a iya mayar masa ba, a wani aikin rashin imani.
A watan Mayun bana, wani jariri dan wata 21 mai suna Musa kishiyar mahaifiyarsa ta cutar da shi a kauyen Gulu da ke karamar Hukumar Rimin Gado a Jihar Kano. Ta yanke harshensa ta karairaya hannunwansa da kafofinsa ta lalata idonsa na dama tare da tsattsaga jikinsa da reza. Musa ya samu kansa a wannan bakin zalunci ne saboda auren iyayensa ya kare an bar kula da shi a hannun kishiyar uwa. Allah Ya kubutar da rayuwarsa bayan an dauke shi zuwa Asibitin Malam Aminu Kano sannan aka koma da shi wani Asibitin kwararru a Abuja.
A watan Afrilun bana ma, an kwantar da wani yar mai suna Anthony Anoke mai shekara 19 da ya fito daga kauyen Amenu Uburu da ke karamar Hukumar Ohaozara ta Jihar Ebonyi, a Asibitin Koyarwa na Abakaliki bayan da kishiyar mahaifiyarsa mai suna Misis Uzoakama Anoke ta watsa masa ruwan batir.
Wata daya kafin haka, wata yarinya mai shekara 10, mai suna Fatima Abdulrashid, an ce kishiyar mahaifiyarta ta sa leda a wuta ta rika diga mata wutar ledar. Fatima, wacce take jinya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya, ta ce bayan da mahaifiyarta ta rasu ne sai mahaifinta ya dauke ta tare da ’yar uwarta daga Zariya ya kai su Gombe don su zauna da kishiyar mahaifiyarsu. Fatima ta ce, “Ta fara hana mu abinci. Dagan an sai ta kulle mu a cikin wani daki da yake kusa da ban-daki na kwanaki. Sai ta rika sanya leda a wuta ta riko tana diga mata wutar ledar a sassan jikinmu. Na ci sa’a da na tsira domin kanwata Narjis ta rasu a sakamakon wannan gallazawa.”
Baya ga rashin aikin rashin tausayi na kishiyoyi, wadansu yara suka shiga mugun halin rayuwa dag alibi suke da alaka da camfe-camfe da maita. Saboda dalilai na son kai da mugunta, bokaye da malaman tsibbu sukan jefa kiyayya a tsakanin iyalai ta hanyar jifar yara da maita.
A watan Janairun bana, an iske wani yaro dan shekara biyu ya kanjame sai kasusuwa bayan da iyayensa suka yar da shi a wani kauye domin ya mutu a huta a kudancin Najeriya.
Yaron wanda yanzu aka sanya wa suna Hope, iyayensa sun yar da shi ne saboda sun dauka shi maye ne, kuma wata Baturiya ’yar kasar Denmark ce ta tsince shi a gefen hanya inda ta dauke shi zuwa asibiti daga nan ta dauke shi a matsayin danta.
Iyaye maza ne manyan masu laifi kan aukuwar haka, domin su ne suke bayar da damar da kishiyoyi ke cin zarafin ’ya’yansu. Don haka akwai bukatar iyaye maza su rika kula da gidanjensu, su rika sanya ido sosai a kan jin dadin rayuwar ’ya’yansu tare da rage mugun kishin da matansu suke nunawa. A shekarar 2003 Najeriya ta amince da dokar kare hakkin yara domin yin aiki da taron duniya kan hakkin yara. Duk da cewa wannan an amince da ita a matakin tarayya, akwai bukatar jihohi a matakansu su amince da ita, kuma zuwa yanzu jihohi 16 ne kawai suka yi hakan daga cikin jihohi 36.
Babu wata kasar da ta san abin da take yi da za ta rika sakaci da makomar yaranta; don haka akwai bukatar a rika yin aiki da dokokin da za su magance matsalolin da yaran da auren iyayensu ya tarwatse da wuce iyaka a takaddamar iyali da amfani da miyagun kwayoyi da kuma safarar mutane.
Su kuma kishiyoyin da aka samu da cin zarafi da tauye hakkin ’ya’yan kishiyoyinsu wajibi ne a gurfanar da su a gaban shari’a a yi musu hukunci domin zama darasi ga saura.
Munanan gallaza wa ’ya’yan kishiyoyi
Munanan hare-hare da kishiyoyi masu mugun kishi da mugunta ke kai wa ’ya’yan kishiyoyinsu ya dauki wani salo mai firgitarwa a baya-bayan nan musamman a…