✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna yin ayyuka ne saboda siyasa ta canja – Shehu ABG

Alhaji Shehu Bawa Garba (ABG), shi ne dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya. A zantawarsa da manema labarai ciki har da Aminiya…

Alhaji Shehu Bawa Garba (ABG), shi ne dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya. A zantawarsa da manema labarai ciki har da Aminiya bayan kammala duba wasu ayyuka a mazabarsa ya ce babu rigima a jam’iyarsu ta APC.

Mene ne makasudin ziyarar da ka kai wasu unguwannin da ke mazabarka?
Alhamdulillah, jifa-jifa in na zo Kaduna nakan ziyarci wuraren da muka ba da ayyuk. Kamar yadda ka sani ba kamar baya ba ne da gwamnati ke ba da kudi ka je ka yi aiki, yanzu dama ce kawai za a ba ka na rubuta wuraren da kake so a yi ayyuka a mazabarka. Ita kuma Ma’aikatar Ayyuka ta Musamman sai ta ba dan kwangila aikin domin gudanarwa. Shi ya sa koyaushe idan na yi wannan zagaye ko na samu dama na yi magana da ’yan jarida nake fadin cewa duk wani aikin dan majalisa idan har aka ga ba a yi ba, to gwamnati ya kamata a rike tunda ita ke ba da ’yan kwangilar. Na fita domin in duba yadda ayyukan ke tafiya in tabbatar cewa an yi su yadda ya kamata. Kamar a Unguwar Rimi rijiyar burtsatse mai aiki da hasken rana muka yi musu, saboda suna wahalar ruwan sha. Muna kuma kyautata zaton wannan zai taimaka musu sosai. Akwai kuma firemaren da muka je, saboda kamfanin Etisalat na taimaka wa makarantu na rubuta sunan makarantar kuma cikin yardar Allah an kammala gyaran ajujuwanta.
Ko ka gamsu da yadda ayyukan ke tafiya musamman wadanda ba a kammala ba?
Mun ziyarci gidan Hakimin Unguwar Shanu, domin kafin gudanar da aikin sai da muka ba da umarnin a fada wa masu unguwanni domin a san wanda ya kawo aikin saboda da saninsu muna da tabbacin cewa za a yi aikin yadda ya kamata. Kamar aikin gina asibitin Unguwar Shanu, gaskiya dan kwangilar ya yi aiki mai kyau, kuma muna kyautata zaton in ya ci gaba da haka aikin zai yi kyau. Za mu gina rijiyar burtsatse na zamani a cikin asibitin da gidan likitoci a asibitin; kuma za mu yi aikin ne a matakai uku. Saboda haka an ce gani ya kori ji ana iya zuwa domin a ga aikin da muke yi a wadannan wurare da na ambata. Da farko a Badarawa muka so gina asibitin, amma saboda rashin fili sai muka kai Unguwar Shanu. Muna sa rai a bana kodai mu nemi fili mu saya, ko mu nemi alfarmar gwamnati a ba mu inda za mu kai aikin da za a yi a Badarawa insha Allah.
Wane kalubale ka fuskanta bayan zabarka a kan wannan kujera?
Daidai gwargwado muna samun hadin kai wurin mutanenmu musamman a karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, da yawa sun san cewa kujerar dan majalisa ba ta zartarwa ba ce, babu wani kasafin kudi da ake bayarwa ga dan majalisa.  Ayyukanmu yin dokoki ne, wasu ayyukan da muke yi, muna yi ne kawai saboda siyasa ta canja. Idan ba ka fito ka aiwatar da ayyukan da mutane za su gani ba, babu abin da ba za a ce ba.  Za ka ji wasu na cewa wai dan majalisa ana biyansa Naira miliyan 200 ko miliyan 500, wanda kowa ya san cewa duk siyasa ne. Kuma abin da ya sa na fita wannan zagaye shi ne yawancin ’yan siyasa idan suka zo kowa neman abin da zai samu yake yi, shi ya sa na ga ya kamata ’yan ayyukan da muke yi mu rika zagayawa domin mutane su san cewa muna yin abubuwan da suke bukata. A cikin ’yan siyasa akwai wadanda muka ba tallafin motoci da kudi. Kwanan nan akwai mutum 50 da muka ba jarin Naira dubu ashirin-ashirin, cikinsu akwai masu tuyan kosai da sauran kananan sana’o’i da muke ganin wannan kudi zai taimaka masu. Haka akwai kungiyoyin addini da muka ba motoci, muna kuma kan yin wannan taimako ne tunda akwai sauran lokaci.
Hukumar zabe ta hana ’yan siyasa kamfe, ba ka ganin zagayen naka wasu na iya fassara shi da yakin neman zabe?
Harka ce ta jama’a kuma jama’a ne suka zabe ni, saboda haka duk da na ce akwai ma’aikatar da ke ba da wadannan ayyuka, ni nasa a yi ayyukan nan kuma a mazabata ake yi. Saboda haka ba wani abu ba ne idan na je domin yi wa mutane bayanin abubuwan da ke gudana a mazabata. Idan muka bari aka yi aikin da bai dace ba, na cutar da mutanen mazabata ke nan, shi ya sa kusan duk mako idan na samu dama zan bi in ga ingancin ayyukan da muka bayar.
Wane kira za ka yi ga jama’ar da aka samar wa wadannan ayyuka?
Kamar a tashar motar Kawo yadda suka yi mana bayani kusan shekara 20 ke nan suke fama da matsalar ruwa, rijiyarsu ma ta kafe a yanzu. Sai ga shi Allah Ya sa ta dalilina sun samu ruwa. Kiran da zan yi masu shi ne yadda Allah Ya sa muka yi masu wannan famfo ko rijiyar burtsatse su kula da shi yadda ya kamata.
Kana ganin jam’iyyarku ta APC za ta iya kwatar mulki a hannun Jam’iyyar PDP, lura da rikicin da ke cikin APC a yanzu?
Babu wata rigima a APC, kai ne ke ganin akwai rigima. Muna nan daram dam kuma kanmu a hade yake, kuma in Allah Ya yarda aka gama shirye-shirye muka tsayar da dan takarar gwamnanmu a jihar nan za mu samu nasara. Kamar yadda ka sani ne a zaben 2011, ’yan majalisar dattawa biyu muka samu kafin a kwace daya a kotu. Wannan karon muna sa ran za mu ci kujerun uku, za mu kara samun ’yan majalisar jiha da na Tarayya kuma muna kyautata zaton mu kai zababben gwamnanmu na APC gidan gwamnati in Allah Ya yarda.
Me ke sanya wasu ’yan majalisa gudun mutane bayan su suka zabe su?
A wasu lokuta matsin da suke samu daga wurin mutane na da yawa, amma kamar ni ina da wani tsari, idan akwai zan ce akwai, in kuma babu zan ce babu. Harkar nan sai kana fada wa mutane gaskiya, wasu kuma ba su son jin gaskiyar. Kuma a yau ko Gwamna kake duk da kudin da ake ba ka, don yin ayyuka akwai lokacin da za a zo babu yadda za ka yi domin bukatu na da yawa. Shi ya sa muke bin mutanen da da lalama. Wanda ya zo nema ka ba shi, in ba ka da shi, sai ka yi masa magana da kalma mai dadi da za ta kwantar masa da hankali.