✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muna son ci gaban Iran — Yeriman Saudiyya

Yerima mai jiran gadon Saudiyya ya yi wasu kalamai masu taushi kan dadaddiyar abokiyar burmin masarautar, wato Iran, yana mai cewa ya nemi “kyakkyawar” alaka…

Yerima mai jiran gadon Saudiyya ya yi wasu kalamai masu taushi kan dadaddiyar abokiyar burmin masarautar, wato Iran, yana mai cewa ya nemi “kyakkyawar” alaka da kasar.

Hakan na zuwa bayan rahotanni sun ce kasashen biyu da ba sa ga maciji da juna sun yi ganawar sirri a kwanakin nan a birnin Bagadaza.

Kasashen biyu, da suke karakainar samun fada a ji a yankin, sun yanke huldar diflomasiyya a 2016 bayan masu Iraniyawa masu zangazanga sun kai hari kan kafofin diflomasiyyar Saudiyyar biyo bayan zartar da hukuncin kisa kan wani jigon malamin Shi’a da Saudiyyar ta yi.

“Iran, makwabciyar kasa ce, abin da muke muradi shi ne kyakkyawar dangantaka kuma mai yauki da Iran,” kamar yadda Yerima Mohammed bin Salman (MBS) ya fada a wata hira da wani gidan telebijin na yankin Gabas ta Tsakiya a ranar Talata.

“Ba ma son lamura su sukurkucewa Iran. Sabanin haka ma, muna kaunar Iran ta habaka… sannan mu taimaka wajen bunkasar yankin da ma duniya baki daya.”

Yeriman ya kara da cewa, hukumomin birnin Riyadh na aiki kafada da kafada tare da kawayen Saudiyyar na yankin da sauran kasashen duniya wajen magance “bakin halayyar”, hukumomin Tehran din yana mai ambato shirin nukiliyar Tehran da ma mara baya ga kungiyoyi ta bayan fage a Gabas ta Tsakiya.

“Muna sa ran shawo kansu tare da kulla kyakkyawar dangantaka da Iran wacce za ta taimaki kowa,” a cewar Yerima Mohammed yayin hirar ta minti 90.

Ana ganin hakan a zaman wani sauyi matsaya idan aka kwatanta da hirarrakin da Yeriman ya yi baya, inda yake sukar Tehran, da zargin cewa hukumomin birnin na rura wutar rashin tsaro a yankin.

Sai dai bai ambaci zama teburin sulhu da Iran din ba. Zaman teburin sulhu a Bagadaza, wanda Firaiministan Iraki Mustafa al-Kadhimi, ya tsara bai fito bainar jama’a ba har sai da Jaridar Financial Times ta ruwaito cewa an gudanar da zaman sulhun a karon farko a ranar 9 Afrilu.

Wani jami’in Gwamnatin Iraki ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP tattaunawar, yayin da wani jami’in diflomasiyya daga kasashen Yamma ya ce an masa karin haske ne gabanin zaman tattaunawar kan yunkurin kyautata dangantaka tare da sassauto da zaman tankiya tsakanin kasashen biyu.