Gwamnatin Zamfara ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya hada ta da masu zuba jari daga kasashen waje, domin sarrafawa da alkinta dimbin ma’adanan da ke jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Daraktan Yada Labaran Ofishin Mataimakin Gwamna, Babangida Zurmi ya raba wa manema labarai a Gusau a ranar Juma’a.
Zurmi ya ce mataimakin gwamnan jihar, Hassan Nasiha ne ya yi wannan kiran, yayin taron masu ruwa da tsaki na harkokin zuba jari da gwamnatin kasar Indiya ta shirya a Abuja.
Ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin Zamfaran na son hada guiwa da su ba a iya fannin sarrafa ma’adinai kadai ba, har ma da sauran hanyoyin bunkasa tattalin arziki.
“A madadin Gwamna Bello Matawalle da al’ummar Zamfara, ina ba ku tabbacin cewa gwamnatinmu a shirye take a koda yaushe domin amsa goron gayyatar kasar Indiya.
“Ba don komai ba, sai don musayar ilimi tsakanin jihar da kasar, musamman a bangaren bunkasar tattalin arziki,” in ji shi.