Kungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa (ARD) sun roƙi mahukunta da su shiga-su-fita don ganin an ceto wata abokiyar aikinsu da aka yi garkuwa da ita watanni takwas da suka gabata.
Reshen ƙungiyar da ke Cibiyar Lafiya ta Tarayya a garin Owo na Jihar Ondo ce ta yi wannan kiran a ranar Juma’a.
- Abba ya naɗa Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida
- Manoma sun dara bayan samun ruwan sama a Taraba
Likitocin suna kira ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kaduna da hukumomin tsaro da su yi duk mai yiwuwa wajen ceto abokiyar aikinsu da aka yi garkuwa da ita tun cikin watan Disamban bara.
Kungiyar ta yi kiran ne a lokacin da take mika bukatun ta ga mahukumta a ranar Juma’a bayan wata zanga zangar lumana da suka yi a garin Owo.
Da yake yi wa ’yan jarida karin haske bayan zanga-zangar da suka gudanar a kan titunan garin Owo, Shugaban kungiyar, Dakta Asunloye Olufemi Adesola ya ce tun a ranar 27 ga watan Disamba na bara aka sace abokiyar aikin tasu amma har yanzu babu amo ballantana labarinta.
Aminiya ta ruwaito cewa, an dai yi garkuwa da Dakta Ganiyat Popoola wadda likitar ido ce da ke aiki a Cibiyar Ido da ke Kaduna tare da mijinta da kuma ’yar kaninta.
Sai dai a cewar Adesola, tun a watan Maris mijin likitar ya shaki iskar ’yanci yayin da kawo yanzu Dokta Ganinta da yar kaninta ke tsare a hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
“Saboda haka muke rokon Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kaduna da Hukumomin tsaron kasa su hanzarta daukar matakin gaggawa wajen ceto Dakta Ganiyat Popoola daga inda ake tsare da ita.”
Dakta Adesola ya ce “Muna bukatar a ceto wannan mata abokiyar aiki ba tare da bata lokaci ba.”
Ya kara da cewa wannan zanga zangar lumana ta kasa ce baki daya domin dukkan ’ya’yan kungiyar da yawun su ake yin wannan fafutukar.