Shugaban Kasuwar Kankana da ke Farar Gada a garin Jos, Jihar Filato, Alhaji Sirajo Bello Bara ya ce a kullum suna samun mutanen da suke zuwa sayen kankana daga Kudancin kasar nan da sauran sassan Najeriya. Alhaji Sirajo Bello ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos, inda ya ce gaskiya harkokin kasuwancin kankana yana tafiya daidai a kasuwar, musamman a wannan lokaci da ruwan sama ya tafi.
Ya ce a wannan lokaci na sanyi ne kankana ta fi zuwa sosai. Kuma an fi noma kankana ne a jihohin Gombe da Bauchi da Jigawa daYobe da Borno.
Alhaji Sirajo Bello ya ce suna samun kankana daga jihohin da ya ambata da kuma jihohin Kano da Sakkwato da Kebbi. Kuma suna samun masu zuwa suna saye daga Kudancin kasar nan da kuma nan Jihar Filato.
“Akalla ana kawo mana mota 25 na kankana a wannan kasuwa a kowace rana. Kuma a kullum ana loda motocin da suke tafiya zuwa garuruwan Fatakwal da Warri da Legas,” inji shi.