✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna maraba da yunkurin samar da wuraren kiwo – Ya’u danfulani

Alhaji Ya’u danfulani, Shi ne Shugaban Kamfanin Fulfulde, kuma fitaccen makiyayi ne a Jihar Kaduna. A tattaunawarsa da Aminiya, danfulani ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta…

Alhaji Ya’u danfulani, Shi ne Shugaban Kamfanin Fulfulde, kuma fitaccen makiyayi ne a Jihar Kaduna. A tattaunawarsa da Aminiya, danfulani ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta samar wa makiyaya filayen kiwo da ta kudiri niyyar yi, sannan ta tallafa musu kamar yadda take tallafa wa sauran bangarori a kasar nan:

 

Aminiya: A matsayinka na makiyayi, yaya kake ganin yunkurin Gwamnatin Tarayya na samar wa Fulani wuraren kiwo na musamman don a zaunar da su wuri daya? 

danfulani: Ai dama mafi yawan kasashen duniya gwamnati ceke kebe wa makiyaya wuraren kiwo inda zas u zauna ba irin kiwonmu wanda kullum suna daukar shanu suna yawo nan gobe su bar nan, jibi su koma can ba. A duk inda ka je a kasashen duniya za ka ga cewa an samar musu da wurare da za su yi noma su yi kiwo su zauna ba a yi ta yawo ba. Don haka alhaki ne na gwamnati ta samar wa Fulani wurin kiwo da makarantun ’ya’yansu da duk irin abin da rai ke bukata na rayuwa. Sannan a samar musu da irin tallafin da ake bai wa sauran kungiyoyi domin su amfana da gwamnati kamar wanda ake bai wa manoma. To da wannan muke cewa gwamnati ta san yadda za ta  yi wa makiyaya, domin hakan zai kara sa musu natsuwa da raguwar tashe-tashen hankula da ake ta fargaba a tsakaninsu da manoma. Kuma idan an yi haka saniya za ta ba da abin da ake so na nama da madara, domin tana huce, sannan ga taki, domin a kasar Indiya da muka je ziyara na ga yadda suke gudanar da kiwo sai abin ya ba ni sha’awa, domin saniya idan ta yi kashi sai ka ga ana bi ana kwashewa, don a inganta shi. Saboda ita saniya Allah Ya yi mata albarka da abubuwa da yawa; ka ga da daya take haifa a shekara, amma in ka dubi irin yadda ake kara-kaina da ita, shanu sun karade ko’ina a kasa, suna samar da nama da mai da madara. Don haka ina goyon bayan gwamnati a kan harkan samar da filayen kiwo ga makiyaya a kasar nan tare kuma da ba su tallafi.

Aminiya: Baya ga kiwo kana da alaka da noma. Yaya ka kalli batun sake farfado da noma da gwamnati ta mai da hankali domin wadata kasa da abinci?

danfulani: Ai Najeriya yanzu a gaskiya kusan kashi 90 na mutane sun rugumi noma da kiwo, kusan duk mutane suna ba da karfi a kansu, domin babu abin da ya fi noma. Ko ba ka da aikin yi idan dai za ka iya noma abin za ka ci kai da iyalanka, to ai ba za ka je ko’ina bara ba, sai ka hakura da abin da Allah Ya ba ka, kuma ya ishe ka kai da iyalinka baki daya. Sannan noma shi ne abu na farko da yake saurin samar da aikin yi ga ’yan kasa, domin yanzu matasa da suka rungumi noma da kiwo a kasar nan ba su da iyaka, kuma suna samun alheri kwarai da gaske. Saboda gwamnati tana ba da tallafin taki da iri mai kyau da maganin feshi da na kwari da sauransu. To kuwa ya kamata a yi noma, don haka mutane suna amfana da harkar noma. Sai dai ina kara ba gwamnati shawara kamar yadda ta kulle duk wata kafa na shigowa da abinci kasar nan, to ta kara dagewa a kai domin mu tsaya da kanmu duk shigowa da wani nau’in abici gwamnati ta tsaya a kan bakanta ta hana shigowa da shi kasar nan.Shi ne kawai magana in ma wahalar ce mu sha ta daga baya mu ji dadi.

Aminiya: Yaya kake ji idan aka ce wa ’yan Arewa cima-zaune bayan nama da abinci daga Arewa suke?

danfulani: A’a ai dan Arewa ba cima-zaune ba ne domin Allah Ya yi wa dan Arewa albarka da kwazo. Saboda in ka duba ba ma Najeriya ba, a Afirka baki daya kusan Arewa ce ke dauke da ita a fannin abinci, sai dai kawai a ce ba su da baki ne na yin gori kawai. Shi ya sa ake hangen cewa ragwage ne domin duk abin da ake ci daga nan Arewa ake samar da shi, to wanda yake samar da abin da za ka ci ka rayu kake ce wa malalaci. To amma yanzu su ma masu fadan sun gane cewa ba haka ba ne.

Aminiya: Duk da arzikin noma da kiwo da Allah Ya albarkaci Arewa, maimakon a samar da kamfanonin da za su rika sarrafa kayan abinci da nama da madara, sai a rika wahalar kai su har Kudu a wulakance, me za ka ce?

danfulani: Ai yanzu shugabanninmu da masu kudinmu na Arewa ya rage gare su, tunda yanzu an samu gwamnatin da take kishi a kan harkar noma, idan  Allah Ya yarda an kusa kaiwa ga haka. Noma da kiwo ka ga yanzu yadda aka fara sarrafa nono, idan an inganta shi haka kayan itace kai har ma da kifi to shi ma nama da su masara da duk wani abu da ake nomawa, nan ba da dadewa ba za ka ga masu kishi sun fara inganta shi suna sarrafa shi tare da samar masa fakiti ana sawa ana fita da shi ana kaiwa inda ya kamata. Ba wai kawai mu muna shan wahala na noma da kiwo tare da samar da duk wani nau’i na abinci ana kai musu su kuma ke  amfana da shi, kuma suna kiranmu malalata ba.

Aminiya: Ko akwai wata shawara da kake son ka bayarwa?

danfulani: Akwai shawara da jan hakali, na farko shi ne gwamnati ta kara kaimi a kan harkar tsaro ta rika bibiyar yadda al’amura suke tafiya kwarai. Sai ku manema labarai ku kara sadaukar da kai kuma ku yi kokarin yin bincike a wajen gudanar da aikinku. Su kuma wadanda aka ba amana su ji tsoron Allah su yi iya kokarinsu wajen tsare amana. Sannan abu na gaba shi ne al’ummar Najeriya gaba daya mu rika hakuri da juna, mu daina kyamar juna, kuma mu rika girmama addinin junanmu tare da sanin makomarmu. To idan kowa ya yarda da haka za a zauna lafiya sannan kuma kasa za ta ci gaba.