✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna kokarinmu wajen samar da zaman lafiya – Janar Buratai

Babban Hafsan Sojin Kasa Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce sojoji suna matukar kokari don magance kashe-kashen da suke faruwa a Jihar Zamfara. Bayan…

Babban Hafsan Sojin Kasa Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce sojoji suna matukar kokari don magance kashe-kashen da suke faruwa a Jihar Zamfara.

Bayan da aka ce masa wadansu jama’a na ganin sojojin sun gaza bisa la’akari da cewa ana garkuwa da mutane duk da cewa sun ce suna kokari.

Sai ya ce, “Duk wanda ya ce sojoji ba sa kokari bai san sha’anin tsaro ba.”

Ya kara da cewa shi tsaro ana fara shi ne daga matakin fako – wato daga kan jama’a.

Janar Buratai ya ce sojoji na iya bakin kokarinsu domin tabbatar da cewa suna kare rayukan jama’ar kasar nan.

An kashe akalla mutum 3,500 yayin da wadansu 9,000 suka jikkata a tsawon shekara biyar, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi ya shaida wa BBC.

Ya ce alkaluma sun nuna cewa kimanin kauyuka 500 ne aka kai wa farmaki, yayin da aka lalata kuma aka bata hekta 13,000 na gonaki.

Farfesan ya ce sun tantance haka ne saboda duk lokacin da ’yan bindiga suka kai hari gwamnatinsu tana tura ayarin kai taimako ga iyalan mamata da wadanda suka jikkata da kuma wadanda suka rasa dukiya.

Ya ce suna ba jami’an tsaro dukkan goyon bayan da ya dace wajen ganin an kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa a jihar.

Idan ba a manta ba, a karshen makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta dakatar da aikace-aikacen hakar ma’adinai a jihar a ci gaba da kokarinta na shawo kan matsalar tsaro.