Gwamnatin Jihar Yobe ta amince da kashe fiye da naira miliyan 100 wajen bayar da abincin buda-baki a wannan wata na Ramadana.
Kwamishinan al’amuran addini da kula da da’a na jihar, Alhaji Yusuf Umar ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Damaturu, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa musulmi marasa galihu kimanin 16,800 ne ke cin moriyar shirin na rabon abincin duk rana a watan na Ramadana.
Aminiya ta ruwaito kwamishinan yana wannan jawabin ne yayin rabon kayan abinci ga wadanda za su rika sarrafa shi da kuma ‘yan kwangila da ke samar da abincin.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta fadada cibiyoyin ciyar da abinci daga 67 zuwa 84 kuma ana sa ran kowace cibiya za ta ciyar da akalla mutum 200 a kullum.
Kwamishinan ya kara da cewar, gwamnatin jihar za ta sa ido sosai kan duk ayyukansu domin ganin an yi abin da ya dace.
Kazalika, ya bukaci masu samar da abincin da su tausaya, kuma su kasance masu gaskiya da rashin son kai wajen rabon abincin.