✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muna kan binciken wadanda suka kona gidan Sarkin Fulanin Oyo – ’Yan sanda

Kwamishiniyar 'Yan Sanda ta Jihar Oyo, Ngozi Onadeko ta yi kira ga jama'ar jihar da su kwantar da hankulansu,

Kwamishiniyar ’Yan Sanda ta Jihar Oyo, Ngozi Onadeko ta yi kira ga jama’ar jihar da su kwantar da hankulansu, tana mai ba da tabbacin cewa suna iya kokarinsu wajen ganin kura ta lafa.

Ta kuma ce tuni rundunar ta fara bincike a kan kone gidan Sarkin Fulanin jihar, Alhaji Saliu Abdulkadir da wani mai suna Cif Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya jagoranta a garin Igangan.

Kwamishiniyar wacce ta yi magana ta bakin kakakin rundunar a jihar, Olugbenga Fadeyi, ta ce ko mutum daya bai rasa ransa ba yayin harin da aka kai ranar Juma’a.

Sai dai rundunar ta amince cewa an sami asarar dukiya mai yawa sakamakon harin, inda ta ce tuni suka fara sintiri a yankunan da abin ya shafa don tabbatar da cewa wani rikicin bai sake barkewa ba.

Ta ce, “Sai dai abin takaicin shine zaman lafiyar da muke riritawa, wasu matasa karkashin jagorancin Sunday Igboho a Igangan sun kawo karshensa da misalin karfe 4:30 na ranar 22 ga watan Janairun 2021.

“A sakamakon haka, hatta jami’anmu sai da aka yi musu ta’adi.

“Muna iya bakin kokarinmu tare da yin taka-tsantsan wajen ganin wutar lamarin ba ta sake ruruwa ba.

“Kwamishiniyar na amfani da wannan damar wajen yin kira ga matasa kan su tabbatar ba a yi amfani da su ba wajen tayar da rikicin kabilanci.

“Babu wani lokaci da rikici ya taba kawo zaman lafiya ko ya magance kalubalen tsaro.

“Mun kama mutane da dama da ake zargi da aikata laifuka iri-iri kamar satar mutane da kuma kisan kai a sassa daban-daban na jihar nan. Mun gurfanar da wasu a gaban kotuna kuma tuni ma har an daure wasu, yayin da wasu kuma muke kan bincike kafin su ma mu gurfanar da su.

“Ina so in tabbatarwa da jama’a cewa jami’an tsaro ba za su zauna su zuba idanu wasu marasa kishin kasa suna daukar doka a hannunsu ba.

“Mun fara bincike a kan ta’asar ta Igangan, kuma za mu ci gaba da yi har sai mun kammala shi tare da hukunta duk wanda aka samu yana da hannu a cikinsa,” inji Kwamishiniyar.

A kwanakin baya ne dai Igboho ya ba dukkan al’ummar Fulani mazauna garin na Igangan kwanaki bakwai kan su tattara komatsansu su bar yankin, inda bayan cikar wa’adin kuma ya jagoranci matasa wajen aika-aikar.

Kazalika, ko a makon da muke ciki sai da Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu shima ya ce ya ba dukkan Fulani makiyaya mako daya su fice daga dazukan jiharsa.