Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta saki mutumin nan mai rajin kare hakkin Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.
Lauyan da ke kare Igbohon, Mista Yomi Alliyu, ya ce an sake shi ne a ranar Litinin domin samun damar zuwa asibiti a duba lafiyarsa.
- Rasha ta gindaya wa Ukraine sharudan tsagaita wuta
- Gostomel: Rasha ta kashe Magajin Gari a kusa da Kyiv
Sakin Igbohon na zuwa ne bayan shafe kwana 231 a tsare a wani gidan yari a Cotonou, babban birnin Jamhuriyyar Benin.
Jim kadan bayan sakin shi, Alliyu ya shaida wa manema labarai cewar, gwamnatin kasar ta amince tare da sakin shi, bisa sharadin zai je a duba lafiyarsa a daya daga asibitocin kasar.
Alliyu ya ce “Ba a saki Igboho ba, an dai ba shi damar ya je a duba lafiyarsa a asibiti.
“A baya na bayyana yadda muke ta shirye-shiryen ganin an sake shi don a duba lafiyarsa.”