Hukumomin Jamhuriyar Benin sun sako madugun masu neman ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Yarabawa zalla, Suday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.
An fara neman Sunday Igboho ruwa a jallo ne bayan ya jagoranci tarzoma da hare-haren da aka kai wa kauyukan Fulani gami da ba su wa’adin ficewa daga yankin Yarabawa da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
A watan Oktoban 2021 jami’an tsaro suka yi musayar wuta na tsawon lokaci da magoya bayan Igboho a lokacin da jami’an tsaro suka kai samame gidansa, inda suka kama makamai da mutum 13 daga cikin yaransa nasa, amma ya tsere.
A lokacin ne ’yan sanda suka sanar cewa sun gano shirin Igboho na kaddamar da tayar da kazamin bore da nufin neman ballewa daga Najeriya.
Sunday Igboho da matarsa baturiya sun shiga kasar Jamhuriyar Benin ne da nufin tsallakawa zuwa kasar Jamus, amma aka cafke shi a can kan zargin alakama da masu aikata manyan laifuka.
A shekarar da ta gabata hukumomin kasar suka ba shi damar kula da lafiyarsa, amma da sharadin ba zai bar kasar ba.
A ranar Litinin ne lauyansa ya tabbatar cewa hukumomin Jamhuriyar Benin sun sako shi.
Babban lauyan gwamnatin Benin, Ibrahim Salami, ya ce, “An sake shi kuma ya fice daga Jamhuriyar Benin,” amma bai yi karin bayani ba.
An ga Sunday Igboho a wani bidiyo yana godiya ga Shugaba Patrice Talon da tsohon shugaban Najeriya da kuma fitaccen marubuci Farfesa Wole Soyinka bisa goyon baya da suka ba shi.