✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matakin Gwamnatin Kano kan Sheikh Abdujabbar ya yi daidai —JNI

“Duk wani Musulmin gaskiya dole ne ya soki dukkan wanda yake kokarin aibata Sahabbai.”

Kungiyar Jama’atul Nasril Islam (JNI) karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ta yaba wa matakan da Gwamnatin Kano ta dauka kan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Idan dai za a iya tunawa, a makon jiya ne Gwamnatin Jihar ta dakatar da malamin daga yin wa’azi saboda abin da ta kira yanayin wa’azinsa wanda zai iya tayar da zaune tsaye.

Babban Sakataren kungiyar Jama’atu, Dokta Khalid Aliyu a cikin wata sanarwa ya soki malamin inda ya ce, “Salon da ya dauka yana kaskantar da darajar Sahabban Annabi (S.A.W) wanda daya ne da taba shi Ma’aikin.

“Zamanin Sahabbai shi ne mafi kyawun lokuta, saboda haka, duk wani Musulmin gaskiya a fadin duniya dole ne ya soki dukkan wanda yake kokarin aibata su.”

Dokta Khalid ya ce “Abubuwan da Sheikh Abduljabbar yake yi ba su da maraba da taba martabar Ma’aiki, wanda ba za mu taba yin sako-sako da shi ba.”

JNI ta kuma ce tana goyon bayan matakin da aka dauka na hana Abduljabbar yin wa’azi a fadin Jihar Kano har zuwa lokacin da za a kammala binciken zarge-zargen da ake masa.

Daga nan sai JNI ta yi kira ga al’ummar Musulmi da su jajirce wajen neman ilimi da fahimtar addini na gaskiya ba tare da bin rudun abin da kungiyar ta kira ‘malaman son zuciya’ ba.