Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce a shirye yake ya shirya da tsohon mai gidansa kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ganduje bayyana haka ne a hirarsa da gidan rediyon Farnasa inda ya ce ’yan jagaliyar siyasa da ba sa son ganin shi da Kwankwaso a inuwa daya ne ke rura wutar zaman doya da manja a tsakaninsu a halin yanzu.
- Mun tara kudin shiga na N2.3trn a bana —Hukumar Kwastam
- ’Yan bindiga sun ya garkuwa da ’yan kasuwa a hanyar Birnin Gwari
“Ka san akwai mutanen da sun saba tayar da kura, amma muna kokarin ganin mun sha gabansu mun sasanta.
“Kowa ya san sulhu shi ne abin da ya fi alheri. Muna addu’a Allah Ya ba wadanda suke kokarin sasanta bangarorin su yi nasara,” inji shi.
Idan ba a manta ba a ranar Talata, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kai wa Sanata Kwankwaso ziyarar ta’aziyyar rasuwarsa dan uwansa, Inuwa Musa Kwankwaso, a gidansa da ke unguwar Bompai residence.
Ziyarar da ta haifar da maganganu a tsakanin masu sharhi da ’yan siyasa a fadin Jihar Kano.
A lokacin ziyarar, Kwankwaso da mukarrabansa ne suka tarbi Ganduje da ’yan rakiyarsa da suka hada da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati da kwamishinoni da manyan jami’an gwamantin jihar.
A lokacin ne Sanata Kwankwaso ya gayyaci gwamnan zuwa wurin kabarin mahaifinsa, Marigayi Musa Saleh Kwankwaso, da ke gidan nasa, inda a nan ma aka yi wa mahaifin addu’a.