✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna da macijiyar amana mai shekara sama da dari shida – Hakimin Kwadom

 Alhaji Muhammad Sani Abubakar  shi ne Hakimin Masarautar Kwadom garin Terawa da  ya kafu sama da shekara dari 600 bayan barowar su kasar Yemen suka…

 Alhaji Muhammad Sani Abubakar  shi ne Hakimin Masarautar Kwadom garin Terawa da  ya kafu sama da shekara dari 600 bayan barowar su kasar Yemen suka ya da zango a Dutsen Bima kafin su iso Kwadom mazaunin da suke a yanzu a yankin karamar hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, kuma sun zauna ne tare da wata Macijiya da suka ce ’yar Amana ce wacce suke kiranta Siti Daiyi da yaren Teranci. Ga yadda tattaunawar sa da Aminiya ta kasance.

 

Aminiya: masu karatu za su so jin cikakken tarihin wannan Masarauta ta Kwadom?

Tarihi ya nuna Masarautar Kwadom an kafa ta ne a shekarar 1375, daga wancan lokaci zuwa yanzu shekara ta 2017 idan ka lissafa zaka ga shekara dari 642 ne zuwa yanzu nine Hakimi na 22, kuma tana da Dagatai 3 amma mu Hakimai ne ba mu kai girman Sarakuna ba, yadda aka samu sunan garin Kwadom kuma an samu sunan ne daga yawan kaurace kaurace da Terawan Kwadom suka yi a baya kafin su zauna a inda suke yanzu, sunan garin Nduk Yebe ma’ana wadatattun Haula saboda mu mawadata ne a wancan lokacin muna Kiwo muna Noma kuma mu Mafarauta ne, garin ya kafu ne a tsakiyar wani Daji da ba komai sai wata babbar Bishiya bushashiya a tsakiyan daji a cikin ta kuma akwai wata katuwar Macijiya a lokacin da suka yarda za su zauna a wajen shi ne sai suka yi addu’oi  suka roki Macijiyar da cewa ke Macijiya za mu zauna anan ba za mu koreki ba kema kar ki koremu za mu zauna ne saboda mu Maharba ne kuma manoma makiyaya saboda mu yi noma mu ciyar da dabbobin mu ba zamu cutar da ke ba kema kar ki cutar damu don haka za mu zauna tare da ke har abada, inda tarihi ya nuna aka samu wannan bishiyar da Macijiyar take a nan aka gina Babban Masallacin Juma’a na kofar fada.

Aminiya: kamar yadda kace Kwadom ta kafu sama da shekara dari 600, kun ya da zango a Dutsen Bima shekara nawa da barowar ku Yemen?          

Da barowar mu kasar Yemen tare da dukkanin Terawa baki dayan mu zuwa yanzu ya kai sama da shekara dari 800, daga Yemen da muka fito mun bi ta Ngazargamu ne sai Borno daga nan sai Dutsen Bima a garin Hinna a nan ne muka rarrabu Haula Haula, a wancan lokacin  da muka rabu sunan Kodong Nduk Yebe wadatattu kenan domin Maharba ne kuma Mafarauta ne masu Tama da masaba ne, a wajen ne muka rabu da yawa aka kafa garuruwan Difa da Gwani da Doho da Hinna da Kurba da Liji da Shinga da sauransu garuruwan Terawwa cikin wadannan haula haula ita Kodong tafi kowacce haula yawan kaurace kaurace.

Aminiya: Yallabai da na shigo fada na ji ana kiran takalma 7 su wanene takalma 7 din nan?

Masu Takalma bakwai a nan sune masu nada hakimi kamar ace King Makers a masarauta kenan masu nada sarki.

Aminiya: Tunda kun kasu haula haula, ya alakar Terawan Kwadom da sauran Terawan da kura rabu da su?

Eh gaskiya muna da kyakkyawar alaka a tsakanin mu. Haula haular da muka kaso gida bakwai ce duk wani Bateri da baya daya daga cikin wadannan hauloli da muke da su to bakon amana ne ba Bateri bane.

Aminiya: Yallabai kamar yadda ka bada labarin Macijiyar amana tun farkon kafuwar wannan Masarauta har yanzu wannar baiwar Allah tana nan ko ta mutu?

Wannar Macijiya dai tana nan har yanzu idan ma ba ita da kanta bane to zuriyar ta ce domin inda kaga Masallacin nan na fada a wancan lokaci anan take da aka gida Masallacin mutane suka yi yawa sai ta yi kaura ta koma can yamma da Kwadom wani kogon Dutse da muke kira Ldeng kunu kuma duk daren duniya idan karfe 12 na dare ta yi zuwa karfe 2 tana fitowa ta zaga gari ta koma muna kuma jin karar ta domin idan ta fito za kaji kamar ana jan sarka a kasa har mutane suke cewa Macijiya mai sarka ta fito kuma ba ta taba kowa wancan amanan dai yana nan tsakanin mu da ita.

Aminiya: A baya lokacin da kuka tarar da Macijiya a cikin Bishiyar nan ka ce kun gaya mata cewa ku jarumai ne wato Mafarauta kuma mayaka a tarihi an taba cin Masarautar ka da Yaki?

A, a, kwarai mu jarumai ne, tarihi ya nuna haka amma ba mu taba yin yaki da kowa ba jarumtakar mu ta farauta ita tafi tasiri domin mun kware wajen yin farauta sannan kuma mu manoma ne na rani da Damina.

Aminiya: Tunda ku manoma ne kuna da waSU wasannin gargajiya da kuke yi?

Muna da wasan gargajiyar mu da muke yi duk shekara bayan amfanin gona ya dawo gida inda muke yin bikin cin sabon amfanin gona wanda muke kira Ngwati Linbari  ana kuma cewa Dahigurmari wato gari ya waye bikin muna yin sa ne a tsakanin watannin Disamba zuwa Fabarairu.

Aminiya: Bayan zuwan ilimin zamani kasar nan ya sa kun canja al’adunku?

A, a, zuwan ilimi bai canja wa Terawa kyawawan al’adun su ba musammam Terawan Kwadom domin daukacin Terawa Mutane ne masu neman zaman lafiya da kowa, su kuma mutane ne masu karbar baki saboda karbar bakin da Terawa suke yi ne yasa har  bakin suke son su fi su yawa.