Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Neja ta ce fannin kiwon lafiyar jihar na fuskantar gibin ma’aikata kimanin 3,000.
Gwamnatin jihar ta danganta matsalar da yadda likitoci da sauran ma’aikatan fannin ke yin kaura zuwa wasu kasashe saboda cigaban da aikin ya samu a can; Sai kuma rashin tsaro, wanda asibitoci ma ba su tsira ba.
- ISWAP Na Shirin Kai Hari Da Sace Mata A Kirismeti
- An kori ’yan sanda 7 daga aiki kan yi wa jama’a kwace
Kwamishinan Lafiya ta Jihar Neja, Dokta Muhammed Makusidi, ya ce, “Inda akan samu likitoci 15 zuwa 20, yanzu bakwai kawai ake da su, sun ragu sosai.”
Kwamishinan ya kara da cewa, wannan ya sa gwamnatin jihar ta amince take biyan albashin ma’aikatan fannin kiwon lafiyar jihar yadda ya kamata.
Ya ce, duk da cewa karancin ma’aikata a fannin kula da lafiya matsala ce da ta shafi kasa baki daya, amma jihar ta rasa matasan ma’aikata wadanda suka tafi ketare.
Ya bayyana wa manema labarai haka ne jim kadan bayan kare kasafin ma’aiktarsa na 2023 a Majalisar Dokokin jihar a Minna, babban birnin jihar, ranar Alhamis.
(NAN)