Shugaba Buhari ya bayyana cewa Najeriya na cikin dokar ta-baci don haka ya umarci Manyan Hafsoshin Tsaro da su magance matsalar tsaro da ke addabar kasar.
Bayan ganawarsa ta farko da sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron a Abuja, Buhari ya gaya musu cewa burin ’yan Najeriya a kansu wajen magance mastalar tsaro babba ne, don haka ya umarce su da nuna kishin kasa a aikin nasu.
- Abu 5 da ke sa masoya batawa a lokacin hira
- Na yi wa mata 50 fyade da fashi a gidaje 100
- Za a girke sojoji mata 200 a hanyar Abuja-Kaduna
“Muna cikin dokar ta-baci saboda haka ku nuna kishin kasa tare da cikakkiyar muya’a gare ta.
“Babu wani sabon abin da ba ku sani ba saboda ku ba baki ba ne, kuma ma ina ciki zan kuma taya ku da addu’a.
“Ina tabbatar muku cewa a matsayina Babban Kwamandan Hafsoshin Tsaro, zan yi duk abin da ya dace don mutane su yaba da aikinku,” inji shi.
Sanarwar da kakakinsa, Femi Adesina ya fitar bayan ganawar, ta ci gaba da cewa Buhari ya yi aklawarin samar wa sojojin kayan aiki da sauran bukatu domin cimma nasara wajen samar da tsaro.
Ya kuma ja hankalin Manyan Hafsoshin Tsaron kan ba wa dakarunsu cikakkiyar kula da muhimmanci, matukar suna son cin nasara.
“Kun san yadda abubuwa suke a 2015 da inda yanzu ake da kuma alkawarin da muka dauka na samar da tsaro a kasa, farfado da tattalin arziki da kuma yakar rashawa; kowannensu babban aiki ne amma mun tabuka,” inji shi.
Za mu magance matsalar tsaro —Irabor
Bayan ganawar, Hafsan Hafsoshi, Manjo-Janar Leo Irabor ya yi alkawarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a Najeriya tare da karawa a kan nasarorin da aka riga aka samu.
Ya shaida wa ’yan jarida cewa, “Mun gana da Shugaban Kasa kuma musa sane da bukatun. A yanzu, alkawarinmu shi ne za mu yi duk mai yiwuwa wajen samar da tsaron rayuka da dukiyoyi a fadin kasar nan.
“A madadin Manyan Hafsoshin Tsaro, na yi alkawrin samar da tsaro da aminci a kasa. Mun yi amanna akwai abin da za kara wajen inganta tsaro a Najeriya.”
Manjo-Janar Irabor ya halarci ganawar ce bayan Ministan Tsaro, Bashir Magashi ya yi masa jagora tare da sauran sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron.
Sauran mahalartan su ne: Babban Hafsan Sojin Kasa, Manjo-Janar Ibrahim Attahiru; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo; da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Vice-Marshal Isiaka Oladayo Amao.