✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna bukatar tallafi daga CBN – Shugaban ’yan canji

A kwanakin baya ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito da wata doka da ta shafi huldar kudi a nan gida da kuma kasashen ketare,…

A kwanakin baya ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito da wata doka da ta shafi huldar kudi a nan gida da kuma kasashen ketare, Aminiya ta zanta da shugaban ’yan canji na Abuja, Alhaji Salisu Umar Garu, a kan yadda al’amarin ke shafarsu da kuma sauran batutuwa. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka?
Alhaji Salisu: Sunana Salisu Umar Garu, ni ne shugaban masu sana’ar canji a nan Abuja, ni mutumin kauyen Auyo ne da ke karamar hukumar Hadejia ta Jihar Jigawa.
Aminiya: Me ya ba ka sha’awar shiga wannan sana’a ta canji kuma tun a yaushe ne ka fara?
Alhaji Salisu: A gaskiya sana’a ni a wurina ba sha’awa ce babban abin da ke sa mutum shigarta ba, kaddara ce, idan Allah Ya kaddara ma ka za ka yi sana’ar sayar da yadi, ko hula to ita za ka yi. Ni a yarintana babu sana’ar da na fi sha’awa kamar ta sayar da goro, amma da ya ke wannan ita ce sana’ar da zan yi, a karshe ita na zo na ke yi yau wajen shekara 20 ke nan.
Aminiya: Wadanne irin matsaloli za ka ce ka fuskanta a wannan sana’ar?
Alhaji Salisu: Gaskiya na samu taimakon Allah kusan zan ce ban fuskanci wata matsala a cikinta ba. ita wannan sana’a babban jarinta shi ne rikon amana da gaskiya, idan ka mallaki wannan, to Allah zai kare ka, sai dai dan abin da ba a rasa ba kamar yadda yake ga ko wace sana’a da ka shiga, to sai ka fuskanci kyashi daga wasu ma’abotanta wasu a zahiri wasu kuma a boye.
Aminiya: Ya batun karo da kudin jabu ko ’yan damfara?
Alhaji Salisu: A gaskiya a kashin ni kaina ban taba fuskantar wannar matsalar ba sai dai a kungiyance, ta bangaren jama’a da mu ke shugabanci idan ya shafi wani daga nan Abuja har zuwa Suleja, mu kan yi hikimar da mu ke yi tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, sai ka ga mun kamasu gabanin su aikata abin, saboda za su bugo mana waya, mu ce da su ba matsala, su ba da adireshin inda suke ko lambar motar da suke ciki, haka za a rika tattaunawa da su har a karshe a samu nasarar kamasu hukuma ta wuce da su, daga mu mun gama namu.
Aminiya: Ya hulda take a tsakaninku da bankuna musamman ma ta bangaren dokoki da a ke kirkirowa ko sokewa?
Alhaji Salisu: A gaskiya su bankuna su ma uwargijiyarsu wato Babban Bankin Najeriya, shi ne kirkiro masu ka’idoji da za su bi. To a ka’idojin nan da a ke kirkirowa wani lokaci sai ya shafemu, wani lokaci har ya shafi masu hulda da mu. Wani lokaci idan su ka kirkiro dokarsu kai da ba ka cikin tsarinma sai ka ga kuskuren, wannan kuma dama haka yake tsari ne na dan Adam ba a raba shi da shi da kuskure.
A kullum ina misali da tsohon Gwamnan Banki Charles Soludo a wajen daidaita farashin kudi, a lokacinsa farashin kudi na daukan tsawon lokaci yana tsaye waje guda, kodayake a wani zubin zai dau mataki da zai sa naira ta yi sama. Wani lokacin kuma ya dau matakin da zai sa ya yiwo kasa, amma dai ya kan dauki tsawon lokaci ya na tsaye a waje guda. To ba komai ba ne ke bashi wannan nasarori sai tuntubar masu ruwa da tsaki a cikin harkar da yake yi gabanin daukan mataki. Ya kan turo wakilai zuwa wajenmu a kai-akai su na tuntubarmu suna mu’amala da mu a boye ko a zahiri don sanin yanayi da kuma halin da a ke ciki a aikace, su yi mana tambayoyi kamar yadda kake yi a yanzu suna bin shago-shago, amma wannan na yanzu ban ji yana hakan. Kuma idan ya yi wani abin ko mu da ba mu yi karatu a fannin ba, ko da ya ke mu na yinsa a aikace, sai mun ga illar al’amarin.
Aminiya: A kwanan nan Gwamnatin Tarayya ta fito da wasu sabbin dokoki, ko za ka bayyana mana su da kuma yadda suke shafarku?
Alhaji Salisu: An kirkiro dokoki masu yawa, misali ta ce kada a fita da kudi da ya wuce dala dubu 10, daga baya ta mayar da shi dala dubu biyar. Ta kuma hana ajiyar kudin kasashen waje a banki wato ba damar a yi ajiyarsa sai dai a dauka. Haka nan a baya mafi karancin kudi da za ka dauka a katin ATM da su ka baka a yayin da kake kasar waje shi ne naira dubu biyar. A dokokin da suka kirkiro na kwanan nan sai suka kayyade shi zuwa dala dari uku kacal a rana, sai kuma dala dubu 30 da suke ba mu sau biyu a mako, sun duk dan kasuwa da ya zo sa ya sai ya bamu tarihin kansa, da lambar tantacewa ta asusun ajiyarsa ta banki wato BbN (Bank berification Number) wanda amfani da shi zai ba da damar sanin ajiyarsa na banki, kodayake daga ba ya sun janye wannan. Sai kuma babban doka da ya fi damunmu tare da abokan huldarmu, wato doka a kan Domicile Account, wanda masu huldar kudi a waje ke amfani da ita kamar wajen biyawa ’ya’yansu kudin makaranta, ko zuwa jinya a kasar waje, da kuma ’yan kasuwa, inda a baya idan su ka sayi kudin waje a wajenmu, sai su sanya shi a asusun ajiyar inda za ta sadaka da asusun ajiyar danka da ke karatu a waje ko mai jinya, ko kasuwa, to yanzu sun soke wannan asusun, ga kuma dokar  hana jigilar kudi mai yawa da shi ma suka kara tsaurarawa.
To ka ga wannan ya nuna ba bu basira a ciki,  idan an yi dokar ne a saboda mu masu hada-hadar kudi, to mu babu ruwarmu ba za ta shafe mu ba saboda mu na da han’yoyin hada-hadar kudinmu na daban. Idan an yi ne saboda masu satar gwamnati, to ai satarsu ba ta dala dubu biyu ba ne ko ta dubu uku, masu kauri suke sata, kila mafi karanci su saci dala dubu dari uku ko dai dari daya.
Aminiya: To ya batun darajar naira bayan kirkiro dokokin?
Alhaji Salisu: To a gaskiya darajar kudin kasarmu ya na karuwa, duk da dai muna asara a bangarenmu, to ba za mu ce aikinsu bai yi kyau ba. Sai dai kira da za mu yi ga babban bankin kasa da ya yi la’akari da asarar da muke yi ya rika bamu tallafi. Ba kuma komi ke jawo mana asara ba illa rashin daidaituwar kasuwa. Za ka sayi dala a kan naira 240 a yau da maraice, washegari da safe sai farashinta ya karye ta koma naira 200, idan ba ka sayar da ita a hakan ba, ba ka da tabbacin ba za ta kara faduwa ba zuwa gobe, ka ga ke nan ga kowa ce dala guda ka yi asarar naira 40 ke nan.
Amma a baya kamar mako uku zuwa wata daya, mukanmu mu na sayanta a kan naira 241 sanna mu yi karin kamar rabin dala daya wajen sayarwa, ba ma kai ribar kashi uku cikin dari da gwamnati ta lamunce mu yi kari, amma sai mu samu riba ba asara irin na yanzu ba. a yanzu dala ta rikice ita da kanta sai ta yi raguwar naira 40 a lokaci guda. Misali a ranar Juma’ar da ta gabata mun sa yi dala a kan naira 203 mu ka sayar da ita 205, wani zubin a karshen yini sai dama ta kai naira 207,  ba mu san abin da Allah zai yi ba a ranar Litiniin idan mu ka dawo kasuwa.
Aminiya: kananan ’yan kasuwa da ke sana’a a gefen tituna sun yi korafin a na kamasu, ko abin ya hada harda ku?  
Alhaji Salisu: Duk da cewa doka ce hana dukkan nau’ukan sana’a a gefen titunan Abuja, amma dai ita wannan hukumar a karkashin Babban Sakatare, ta tsaurara duk da cewa da shi a ka yi gwamnatin baya lokacin da minista ne ke kai. Sai dai dama wanda ke matsayin ministan na Abuja a yanzu dama ya nuna mana alama tun a farko, saboda ya nemi ganawa da jama’armu to ayayin ganawar sai ya ce ya ya bai ga ’yan kabilarsa ta Ibo ba a cikinmu.
Mun sanar da shi cewa sana’ar canji ga Hausawa tamkar harkar sayar da kayan gini ne ko kemis ga ’yan kabilar Ibo mu kadai ne ke yinta, su ne ba su kawo kansu ba. A nan ya nuna mana bai ji dadin al’amarin ba, sannan ya ce mu saurari hukuncinsa, daga nan ne a ka rika kama mana mutane, har ma ya zo da kansa inda a lokacin ya sa a ka rusa mana masallaci.