✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna bukatar sojoji su kare layukan dogo a Najeriya — Amaechi

Za a gina layukan dogo daga tun daga Kaduna zuwa Kano kuma ya ketara Maradi.

Ministan Sufuri na Najeriya, Chibuike Amaechi, ya yi kira ga Rundunar Sojin kasar da ta samar da tsaro ga ma’aikata masu gina layin dogo wanda za a fara nan ba da jimawa ba.

Gwamnatin Tarayya ta shirya fara gina layukan dogon daga Kaduna zuwa Kano, Kano zuwa Maradi da kuma na Maiduguri zuwa Fatakwal.

Amaechi ya yi kiran ne a ranar Juma’a yayin da ya ziyarci Babban Hafsan Sojin Kasa, Manjo-Janar Farouk Yahaya, a ofishinsa da ke Abuja.

Ya ce aikin gina layin dogon Kaduna zuwa Kano an tsara za a fara shi ne wani lokaci a cikin watan nan yayin da na Kano zuwa Maradi da Maiduguri zuwa Fatakwal za a fara shi a watan Yuli.

A cewarsa dole ce ta sa bukatar sojojin sakamakon kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta.

Sannan kasancewar sojin zai kara wa ma’aikatan karkashin aiki tare da bai wa kwarorin kwarin gwiwar cewa akwai tsaro a Najeriya.

Da yake mai da martani, Babban Hafsan Sojin Kasar, ya jinjina wa ministan kan ziyarar.

Sannan ya tabbatar masa da cewa rundunar a shirye take ta ba da taimakon da ake bukata domin samun nasarar aikin gina layukan dogon a duk fadin kasar.