Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ce rundunar na bukatar akalla Naira biliyan 24 da miliyan 800 duk shekara domin zuba wa ababen hawansu mai.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da ayyukan da rundunar ta yi da kuma kare kasafinta na 2021 a gaban Kwamitin Ayyukan ’Yan Sanda na Majalisar Wakilai ta Tarayya.
- Za a yi wa ‘yan sandan da aka kashe a zanga-zangar #EndSARS karin girma
- EndSARS: An janye ’yan sanda masu kare manyan mutane
Mohammed ya ce babban tarnakin da hukumar ke fuskanta shine na karancin kudaden gudanarwa sakamakon rashin ware musu isassu a kasafin kudin.
A cewarsa, “Babbar matsalar ita ce abinda aka ware mana ba zai ishe mu gudanar da ayyukan mu tsawon shekara guda ba.
“Alal misali, idan ka dauki iya zuba mai kawai, motocinmu kan sha na kimanin Naira biliyan 22.5 a iya shekara kawai.
“Idan ka hada wadannan alkaluman, iya mai kadai ka ga ya kusan lakume abinda aka ware mana, ba a ma zo bangaren gyare-gyare ba. Idan muna son kula da ababen hawanmu, muna bukatar akalla sama da Naira biliyan takwas a shakara daya kawai,” inji shi.
Ya ce halin tsaron da ake fama da shi musamman a yankin Arewa Maso Gabas da kuma annobar COVID-19, da zanga-zangar #EndSARS da ta jawo kone ofisoshin jami’ansu da dama na cikin tarin kalubalen da rundunar tasu ke fuskantar.
Babban sufeton ya ce a kudin da aka ware musu a kasafin 2021 na Naira biliyan 469.4 an zaftare shi zuwa Naira biliyan 449.6.
Shugaban kwamitin ‘yan sandan na majalisar, Usman Bello Kumo ya ce, “Babu yadda za a yi Naira biliyan 11 ta ishi rundunar a tsawon shekara guda kasancewarta hukumar tsaro mafi girma a kasa.”