Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya nemi goyon bayan Gwamnatin Birtaniya a fannin dakile wasu matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu, waɗanda suka haɗa da garkuwa da mutane, ta’addanci, fashi da makami, satar mai da sauransu.
Ribadu, wanda ya jagoranci taron tattaunawa karo na biyu kan haɗin gwiwar tsaro tsakanin Birtaniya da Najeriya a ranar Laraba, ya bayyana cewa tattaunawar na cikin wani muhimmin mataki na magance matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta da kuma karfafa tsaro a yankin Afirka da ma duniya baki ɗaya.
- An dakatar da lakcaran da ya sa dalibai gwale-gwale a Kano
- Sarkin Kano: An bukaci majalisa ta dawo da Sanusi II
Aminiya ta ruwaito cewa, an gudanar da taron tattaunawar karo na farko a birnin Landan daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 2 ga Fabrairun 2022, wanda Ribadu da sauran manyan jami’an tsaro suka halarta.
Da yake jawabi a wajen taro na Abuja, Ribadu ya bayyana cewa, la’akari da halin da duniya ke ciki a wannan zamani mai cike da sarkakiya, tilas ne a jaddada muhimmancin haɗin gwiwa mai karfi da musayar bayanai a tsakanin kasashe.
A cewarsa, ya zama wajibi ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro ya yi nazari sosai kan yadda barazanar tsaro ke tasowa tare da gano sabbin dabaru domin magance su yadda ya kamata.
Ya nanata cewa daɗaɗɗiyar alakar da ke tsakanin Burtaniya da Najeriya ta ginu ne a kan dabi’u na mutunta juna da kuma buri na samar da tsaro da zai tabbatar da amincin rayuwar duniya.
“A irin wadannan tarukan ne za mu sake tabbatar da kudurinmu na haɗin gwiwa wajen tunkarar duka wata barazanar da ta kunno kai, da daidaita tsarin tsaro da inganta rayuwar al’umma, da kiyaye ka’idojin dimokuradiyya da ’yancin dan Adam, da bin doka da oda.
“A yayin tattaunawar, an cimma yarjejeniya da dama waɗanda suka shafi hanyoyin karfafa haɗin gwiwa a fannonin tsaro, dakile ayyukan ta’addanci da masu tsatsauran ra’ayi, da fataucin kuɗaɗen haram tare da inganta tsaron teku da dai sauransu.
“Saboda haka ya dace a tantance matakan aiwatar da yarjejeniyar da kasashen biyu suka ƙulla.
“Har ila yau, yana da muhimmanci a sake nazarin kan duk wasu matakai domin gano wuraren da ke buƙatar fifiko a halin yanzu bisa la’akari da batutuwan da ke ci gaba da wanzuwa da kuma manyan manufofin kasa,” inji shi.
Ribadu ya kara da cewa, tattaunawar ta kuma buɗe kofa ta musamman da za ta karfafa haɗin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu a fannonin tsaro daban-daban, da suka haɗa da inganta karfin soji, musayar bayanan sirri, yaƙi da ta’addanci, tsaron teku da kuma na yanar gizo.
A nasa bangaren, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na Burtaniya, Tim Barrow, ya ce kasarsa na aiki ne kan tsari na ƙulla alaka ta mutuntawa da goyon bayan juna, tare da ɗaukar ƙudurin ba da gudummawa ta musamman domin inganta tsaro da zaman lafiyar da zai kawo kwanciyar hankali a duniya.
Mista Barrow, wanda mataimakiyarsa Dame Sarah Macintosh ta wakilta, ya bayyana cewa, kasashen biyu za su iya inganta alakar tsaro ta hanyar wannan haɗin gwiwar da kuma tattaunawa da za su taimaka wajen cimma manufofinsu.
Ya ce, “Birtaniya ta himmatu sosai wajen sada zumunci da haɗin gwiwarmu da Najeriya kuma muna gode muku bisa jajircewar ku kan wannan kawancen.
“Haka kuma ni kaina ina alfahari da kasancewa ta cikin sahun masu taka rawar gani a wannan bangare na karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
“A yayin da kalubalen tsaro ke karuwa a duniya, yana da matuƙar muhimmanci mu tallafa wa abokanmu don tabbatar da zaman lafiyarmu a duniya.
“A wannan makon mun sake jaddada aniyarmu ga Najeriya, bisa ci gaban da aka samu tun bayan tattaunawar da aka yi tsakanin kasashen biyu kan haɗin gwiwar tsaro, tun daga yaƙi da ta’addanci da kuma murkushe masu tsattsauran ra’ayi zuwa kare kai daga hare-hare ta yanar gizo.
“Ina kuma miƙa godiyata ga Gwamnatin Najeriya bisa haɗin kan da suke ba mu, kuma ina fatan za mu ci gaba da zurfafa alakarmu a dukkannin kudurori da muradunmu,” in ji shi.