✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna binciken kisan fararen hula harin jiragen yaki a Zamfara —Sojoji

Hedikwatar Tsaro ta ce har yanzu Gwamnatin Zamfara ba ta tuntube ta kan zargin mutuwar fararen hular ba

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce ta fara bincike kan zargin kisan fararen hula a luguden wuta da jiragen yaki suka yi wa ’yan ta’adda a Jihar Zamfara.

Daraktan Yada Labarai na Hedikwaar Tsaro, Manjo-Janar Musa Danmadami, ya ce hadafin harin jiragen yakin na ranar Lahadi shi ne dandazon ’yan bindiga da suka kai hari bisa babura a kauyen Mutumji da ke Karamar Hukumar Maru ta jihar.

“Mun kaddamar da bincike domin tabbatar da gaskiyar rasuwar fararen hula da abin ya ritsa da su  da kuma yawansu.

“A halin yanzu ba za mu iya cewa ga adadin ba, domin kada mu kawo cikas ga binciken da ke gudana.

“Jiragen sun yi luguden wutan ne kai-tsaye a kan ’yan ta’adda kuma an hallaka da dama daga cikinsu,” in ji shi.

Sai dai rahotanni daga jihar sun ce fararen hula 60 sun mutu a sakamakon luguden wuta da jiragen yakin suka yi.

A kan haka ne Manjo-Janar Danmadami ya shaida wa ’yan jarida a ranar Alhamis cewa Hedikwatar Tsaro ta kafa kwamitin bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

Amma ya ce har yanzu ba su samu wata sanarwa ko alkaluman fararen hulan da rahotannin ke cewa jiragen yakin sun kashe ba daga Gwamnatin Jihar Zamfara.

Da yake jajantawa game da sojojin kasa da suka kwanta dama a cikin makonni uku da suka gabata, kakakin Hedikwatar Tsaron ya zargi wasu kafafen yada labarai (ba Aminiya ba) da kara gishiri a labarin.

Nasarorin sojoji

Ya kara da cewa a cikin mako ukun da suka wuce, sojoji da ke yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas sun kashe mayakan Boko Haram da ISWAP 103, sun cafke wasu 40 kuma sun kubutar da mutum 30 daga hannunsu.

A Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya kuma, sojoji sun kashe ’yan ta’adda 60 sannan suka cafke wani dillailin makamai da suke nema.

Ya ce dubun dillalin makaman ta cika ne bayan ya tsaya shan mai a Karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna, inda aka kama bindigogi kirar AK-47 guda biyar, hasrsasai 4,000, hayaki mai sa hawaye da kuma wukaken soja a hannunsa.

ِA yankin Kudu maso Gabas kuma, sojoji sun lalata haramtattun matatun mai guda 57, da wurin fadawa guda 953, kwalekwalen 68 da tankunan ajiyar man sata guda 172, baya ga rijioyin boye man sata 149.