✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna binciken gwamnan Zamfara kan N70bn —EFCC

EFCC ta ce tana binciken Gwamna Bello Muhammad Matawalle na Jihar Zamfara, kan zargin badakalar Naira biliyan 70.

Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta ce tana gudanar da bincike kan Gwamna Bello Muhammad Matawalle na Jihar Zamfara, kan zargin badakalar Naira biliyan 70.

Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ya sanar da haka, tare da cewa hukumar na tsare da tsohon Ministan Wutar Lantarki, Sale Mamman, kan badakalar Naira biliyan 22.

Bawa ya sanar cewa EFCC na binciken Gwamna Matawalle ne, kwanaki kadan bayan gwamnan a bukaci hukumar da ta daina matsa wa gwamnoni da bincike ta mayar da hankali kan ministoci da jami’an fadar shugaban kasa.

Amma a martanin Bawa, ya bayyana cewa hukumar na binciken mutane daga kowane bangare da kuma matsayi.

A cewarsa, abin da zai sa mutun ya fada komar hukumar shi ne aikata almundhana, kuma Matawalle ba shi da shi da hurumin da zai zaba wa hukumar mutanen da za ta yi bincike a kansu.

Aminiya ta ruwaito Gwamnatin Tarayya na cewa Gwamna Matawalle yana da ’yancin fadin ra’ayinsa na neman EFCC ta binciki jami’an da yake ganin suna cin rashawa a Fadar Shugaban Kasa da kuma ministoci masu barin gado.

Gwamna Matawalle a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, “Ina so shugaban EFCC ya yi irin wannan gayyata ga jami’an Fadar Shugaban Kasa da kuma mambobin majalisar zartarwa ta tarayya, wadda ita ce mafi girman matakin gwamnati a kasar nan.”

Da aka nemi jin ta bakinsa, Lai Mohammed ya ce, “Gwamna na da ’yancin bayar da shawarwari, ra’ayinsa ke nan.”