✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna ba da tallafin Naira biliyan daya kan aikin Hajji duk shekara – Gwamna Masari

Gwamnatin Jihar Katsina tana kashe sama da Naira biliyaa daya wajen tallafa wa jin dadin alhazan jihar duk shekara. Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari…

Gwamnatin Jihar Katsina tana kashe sama da Naira biliyaa daya wajen tallafa wa jin dadin alhazan jihar duk shekara.

Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Bello Masari ne ya ambaci haka a ranar Larabar makon jiya a dakin taro da ke ofishins wajen kaddamar da mambobin Hukumar Gudanarwar Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar. Gwamna Bello Masari ya ce, kasancewar kashi 99 na al’ummar jihar Musulmi ne babu laifi don an kashe kudi wajen ayyukan addini a jihar.

Gwamna Masari ya ce maniyyata ’yan boko ne suka fi yawan tsagwammar gwamnati ta hanyar biye wa korafe-korafen matansu yayin gudanar da aikin Hajjin. Ya ce, “Duk koke-koken da ake yi mafi yawa babu hujja. Mutumin da zai yi tafiyar kilomita biyar don ya sayar da nono ko ya saro itace, matsalar ba daga mutananmu na kauye take ba, daga gare ku ne da iyalanku. Aikin Hajji ba yawon hutu ba ne, shi ya sa aka ce sai kana da lafiya tare da guzuri. A tuna irin yadda magabata suka aiwatar da aikin Hajjinsu kuma a wajen neman duniya ana shan wuya balle neman aljanna.”

Gwamna Masari ya yi fatan jami’an da aka dora wa alhakin kula da mahajjatan za su sadaukar da jin dadinsu ga mahajjatan da za su kula da su.

Gwamna Masari ya kuma ja hankalin malamai su rika yin wa’azinsu a kan abin da ya shafi aikin Hajji domin shi ne abin da maniyyatan suke da bukata ba wani abu daban ba.

Ya yi fatan mahajjatan jihar za su yi wa Shugaban Kasa addu’ar karin samun lafiya da kuma ci gaba da samun zaman lafiya a jiha da kasa baki daya.

Da yake jawabin godiya, sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar, Alhaji Salisu Ado Shinkafi, Bunun Katsina ya tabbatar wa Gwamnan cewa, za su yi aiki tukuru ta yadda ba za su ba gwamnati da maniyyata da al’ummar jihar kunya ba.

Shugaban ya ce, “A can baya mun yi aiki a matsayin kwamiti, amma yau ga shi Gwamna ya mayar da mu hukumar gudanarwa saboda haka za mu aiwatar da aikinmu yadda ake bukata tun daga nan gida har zuwa Kasa Mai tsarki.”

Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Mannir Yakubu ne Amirul Hajjin Jihar sai Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Abubakar Yahaya Kusada na cikin ayarinsa.