✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muna asarar miliyoyin Naira duk mako —Dillalan Shanu

Safarar shanunmu zuwa Kudu ba tare da samun matsala ba shi ne babban kalubale.

Dillalai daga garin Nguru da ke Jihar Yobe sun koka da yadda suke tafka asarar miliyoyin Naira kan yadda shanunsu ke mutuwa a yayin safararsu zuwa Kudu.

Hakan dai na faruwa ne sakamakon tsawon kwanakin da ake dauka wajen safarar dabbobin zuwa inda ake kasuwancinsu sakamakon rashin hanyoyin sufuri masu kyau da ababen hawan da ke daukar shanun ke fuskanta.

Yayin zantawa da Aminiya a Babbar Kasuwar Nguru, daya daga cikin dillalan shanun, Alhaji Muhammad Dauda, wanda aka fi sani da Alhaji Tiyal, ya ce daga cikin kalubalen da suke fuskanta a Kudancin kasar nan sun hada da kashe mutanensu da shanunsu.

Ya ce suna tafka asarar miliyoyin Naira saboda rashin kyan titunan da ake bi wajen kai shanun Kudu.

A cewarsa, sukan yi nasarar sayen shanunsu tare da shirya su tsaf don yin jigilarsu zuwa yankin Kudu, amma rashin kyan hanya na sa wasu daga cikin shanun su kwanta rashin lafiya, wasu lokutan ma su mutu.

“Wannan ita ce babbar matsalarmu a wannan sana’a.

“Yankin Kudu ya kasance daya daga cikin manyan wuraren da aka fi sayen shanunmu.

“Amma safarar shanun zuwa can ba tare da samun matsala ba shi ne babban kalubale.

“Makon jiya saniyata daya ta mutu, yanzu ga wata a kwance ba lafiya.

“Ba mu da wani zabi face mu yanka ta kuma dole ne farashinta ya sauka.

“Wannan shi ne abin da muke fuskanta kusan kullum.

“Wurin da ya fi hadari shi ne Jihar Neja. Duk wanda zai kai shanunsa Kudu idan har ya wuce Jihar Neja lami lafiya to ya gode wa Allah.

“Da zarar ka wuce nan, to ana sa ran za ka kai shanunka Kudu ba tare da ka yi asara ba.

“Sama da shekara bakwai, ba ma bin hanyar Birnin Gwari da Tegina. Yanzu mun fi bi ta Lambata da Bida, amma su ma hanyoyin ba su da kyau,” inji shi.

Ya ce ya shafe sama da shekara 15 yana wannan kasuwanci, kuma ya ce har yanzu shi ne babbar hanyar rufin asirinsa, inda ya ce a yanzu ya fi sayen shanu daga Jamhuriyar Nijar saboda sun fi arha a can.

Ya ce, “Daga nan mukan kai shanu zuwa Legas da Isheri da Ibadan da Ilorin.

“Wasu daga cikinmu suna kai nasu Lokpanta da sauran yankunan Kudu maso Gabas.

“Amma wasu lokuta a wasu kauyukan Kudu, muna fuskantar babban kalubale.

“Wasu suna kashewa ko kone mana shanu kuma su kashe mutanenmu.”

A cewarsa, tirela 10 zuwa 15 makare da shanu ke tafiya Kudu duk mako daga yankin.

“Wannan ya faru ne sakamakon faduwar damina. Amma a lokacin rani, muna daukar tireloli sama da 30 daga nan zuwa Kudu.

“Gaskiya wannan harka tana samar wa mutane da yawa aiki, don haka ya kamata a duba halin da muke ciki,” inji shi.

Shugaban dillalan shanun na Nguru, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gyara hanyoyin domin inganta harkokinsu da kuma samar da ayyukan yi ga ’yan kasa.