Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Borno, Mohammed Mustapha, ya ce sun yi wa mambobi da magoya baya sama da miliyan biyu rajistar jam’iyyar a Jihar.
Shugaban ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Maiduguri ranar Lahadi cewa yanzu jam’iyyar na samun karbuwa sosai a Jihar.
- NDLEA ta kama matafiyin da ya boye Hodar Iblis a gaban shi
- Jirgin farko dauke da maniyyatan Gombe 508 ya tashi zuwa Saudiyya
Mohammed ya ce sun shirya tsaf domin su ba sauran jam’iyyu mamaki a dukkan zabukan da ke tafe a 2023.
Ya ce, “Mun tsayar da ’yan takara a dukkan mukamai a Jihar Borno, kuma muna da shugabanni tun daga matakin mazaba har zuwa Jiha wadanda za su wayar da kan masu zabe.
“Ban da dan takararmu na Shugaban Kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, muna da dan takarar Gwamna da na Sanatoci guda uku da na ’yan Majalisar Wakilai guda 10 da kuma na Majalisar Jiha guda 28 a Borno.
“Mun shirya tsaf domin ba ragowar jam’iyyu mamaki da mambobinmu da magoya baya sama da miliyan biyu,” inji Shugaban.
Mustafa ya kuma jinjina wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) saboda kara wa’adin sabunta rajistar zabe, inda ya yi kira ga al’ummar Jihar, musamman matasa da su shiga a dama da su. (NAN)