✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun yi murna da tumatirin dangote

Mun yi murna da tumatirin dangote Edita Hakika mu talakawan Najeriya mun yi farin ciki da matakin da Aliko dangote ya dauka na kaddamar da…

Mun yi murna da tumatirin dangote

Edita Hakika mu talakawan Najeriya mun yi farin ciki da matakin da Aliko dangote ya dauka na kaddamar da kamfanin sarrafa tumatir a Jihar Kano wanda hakan ba karamin abin farin ciki ba ne, musamman idan muka duba muhammancin kaddamar da kamfanin ta fanin tattalin arzikin Najeriya. Masana’antar sarrafa tumatir za ta taimaka wajen rage dogaro ga kasashen waje don sawo tumarin gwangwani. Kuma za ta taimaka wajen rage masu zaman banza da marasa aikin yi. Manom za su amfana cikin sauki ba tare da sun sha wahala ba.
Kuma zai taimaka wa gwamnatin Najeriya dama ta Jihar Kano wajen samun karin kudin shiga musamman a yanzu da darajar man fetur ta fadi a kasuwar duniya. To wadannan kadan ne daga cikin alfanun da za mu samu daga wannan masana’anta da dangote da ya kaddamar a jahar Kano. Sai kuma makwafciyar Jihar Kanon wato Jihar Jigawa, inda acan ma Dangoten ya dauki matakin habaka noman shinkafa gami da sarrafata a Jihar Jigawa, wanda hakan ba karamin ci gaba ba ne, kuma hakan zai yi matukar taimaka wa tattalin arzikin Najeriya. Ina kira ga Gwamnatin Shugaba Muhammadu
Buhari data bai wa wadannan shirye-shirye na Aliko dangote goyon baya dari bisa dari domin ceto tattalin arzikin Najeriya daga halin da yake ciki a yanzu na tabarbarewa. Daga Salim Abubakar Imam Jingir dalibi a tsangayar nazarin tattalin arziki a jami’ar musulunci dake Katsina kuma Shugaban kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Filato 08067922200. [email protected].

Hattara ’yan siyasar Kano  
Ba fada ba da Malam tsakar dare!. Assalamu alaikum. Ina rokon Allah ya sa rayuwar jaridar Aminiya ta nan gaba tafi ta baya albarka. Edita ina son ka ba ni dama inyi kira ga ’yan siyasar Kano, mussamman ’yan Jam’iyyarmu ta APC mu gane cewa, kaso 70 cikin 100 na masoya wannan jam’iyya a Jihar Kano sun samu ne ta dalilin Tsohon gwamna, kuma sanata a yanzu, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso. Mu ’yan Buhariyya zallah mun san haka, duba da irin nasarorin da tafiyarmu ta Janar Buhari ta samu bayan shigowar Kwankwaso wannan tafiya. Mai girma Gwamna Abdullah Umar Ganduje wallahi ka yi hankali da su Shekarau don suna so su yi amfani da kai ne, su cimma manufofinsu. Kowa ya san makiya Buhari ne, ko ma mu ce makiya Najeriya ne su. Daga karshe ina kira da ’yan uwa cewa, kowa ya natsu don gudun da na sani. Daga Abdurrazak Saleh Inuwa (Bala Tudun-Murtala) karamar Hukumar Nasarawa Jihar Kano 08032117371,08095272721

Kira ga yan’uwa Musulmi
Salam Edita gaisuwa da fatan alhairi ina kira a kan dukkan Musulmin duniya da mu kasance masu fadin alkhairi ga shugabanninmu da kuma addu’a tagari a kansu. Domin shi zai kara sa wa su kasance nagari, kuma mu ga ci gaban kasar mu, amma in muka tsine musu ko fadin sharri a kansu tamkar muna kara lalata komai ne; imma ba za ka iya yi musu fatan alkhairiba, to mu yi shuru! Domin fadin Hadisin nan da yake cewa, ka fadi alkhairi ko ka yi shiru. Allah ya sa mu dace amin. Daga T. Bakura  07033572704

Addu’a ga Shugaba Buhari
Salam don Allah Edita ka mika min sakon fatan alkhairi ga jagora nagari, abin koyi Shugaba Muhamad Buhari. Allah ya kara masa tsawon kwana, mu kuma Allah ya ba mu ikon ci gaba da taya shi da addu’a amin. Daga Yusuf Isah Dada Edo Benin

Kira ga Shugaba Buhari
Salam, Edita, ina so ka ba ni dama in yi kira ga Baba Buhari ya dubi halin da direbobi suke ciki, wurin yin takardu, zuwa lasisi kudin sun yi yawa, ga ba kudi. Baba a duba mana. Nagode. Daga Bashiru Aliyu Yuli Wase  

Kira ga Gwamna Ganduje
Salam Editan Aminiya jarida mai farin jini ka mika min sakona ga Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya yi wa Allah da Annabinsa ya karasa mana hanyar da Kwankwaso ya faro daga Makarfi zuwa Sabon layin Hago tsakanin Sabon layin  Hago da Rogo ba karamar lalacewa ta yi ba, mu talakawan wajen ta zame mana tarkon hadari in ruwan sama ya sauka. Allah ya sa sakona ya kai gun da za a share min hawaye.   Daga Yakubu Abdullahi Fulatan karamar Hukumar Rogo Jihar Kano/08098686893

A kare hakkin mata
Aminiya ta 4|3|2016 shafi na 6  na karanta yadda wata mata a Jihar Gombe ta ci zarafin ‘ya’yan kishiyarta har sai da na zubar da hawaye. Ya kamata kungiyoyin kare hakkin mata da yara kanana da lauyoyi mata da ministar mata su tashi domin sauke nauyin da Allah ya dora musu. Daga Maryam Zubairu Garabasa Kazaure

Kira ga Gwamna Bagudu
Assalamu alaikum. Fatan alheri a gareku Allah ya kara yi muku jagoranci, amin. Bayan haka don Allah ku ba ni fili a wannan amintacciyar jarida taku, don in yi kira ga mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu da ya yi wa Allah ya gyara mana hanyar da ta tashi daga kwanar Gayi ta bi ta Diggi, ta zarce zuwa Maidahini kamar yadda ya yi mana alkawari lokacin yakin neman zabe. Domin kuwa hanyar ta lalace matuka.  Daga Muhammad Bello Banganna, karakmar Hukumar Kalgo, Jihar Kebbi

Ga Alhaji Aliko dangote
Edita ba ni fili in mika godiyata ga attajirin nan mai tausayi, Alhaji  Aliko dangote kan taimakon da yake yi wa al’umma, Mun gode, Allah ya saka da alheri, amma ina rokon shi kan ya kirkiro da gidauniyar lafiya  mai kula da rashin lafiya, wacce za ta rika biyan  kudin maganin marasa karfi da marasa galihu, masu bukatar taimako. Daga  Amiru Isah Bakori 07068147933

Jinjina ga Gwamna Masari
Assalamu Alaikum, Edita ka ba ni dama inyi jinjina ga Gwamna Aminu Bello Masari (Dallatun Katsina) bisa ba da gyaran ruwan famfo a garin Malumfashi, tabbas abin a yaba ne ganin yadda al’ummar wannan gari suka dade suna bukatar a gyara musu. Allah ya saka da alkhairi ya ida mashi nufi. Daga Abdulmalik Bello me sai da Engine oil cikin tasha Malumfashi