Kungiyar Malamai ta Najeriya (NUT) ta ce ta yi asarar mambobinta kusan 800 a rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Shugaban NUT, Dokta Nasir Idris ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja a karshen makon da ya gabata.
- United za ta maye gurbin Solskjaer da Brendan Rodgers
- Maciji ya sare shi a hanya bayan ya gudo daga hannun masu garkuwa da shi
Ganawarsa da manema labarai na zuwa ne bayan sace wani Mataimakin Shugaban wata makarantar sakandire a Abuja.
“Zan iya cewa a halin yanzu mun yi asarar malamai kusan 800 a Arewa maso Gabas.
“A yankin Arewa maso Yamma kuma ana ci gaba da garkuwa da malamai da dalibai a sakamakon matsalar tsaron da ake fuskanta a yankin.
Ya kara da cewa, “ba wai ana kashe malaman bane a yankin, a’a satar malaman da neman kudin fansar da ake yi ta yi yawa, saboda galibi wasu malaman sukan ce ba za su bari a dauke daliban su kadai ba sai dai su ce a hada da su.”
Ya nemi gwamnati ta samar da ingataccen tsaro a dukkanin makarantu da ke fadin kasar, lamarin da ya ce muddin ba haka ba kungiyar na iya sanya mambobinta a yankunan biyu da su janye ayyukansu.
Kazalika, ya roki Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta tabbatar da kudirin dokar tsawaita shekarun aikin malaman makaranta zuwa 40 da kuma ritaya bayan mutum ya kai shekara 65.
A cewarsa, malamai da dama na barin koyarwa sakamakon halin ko-in-kula da Gwamnatin Tarayya da Jihohi da ma wasu Kananan Hukumomi ke yi ga malaman musamman na Firamare.
Ya kara da cewa, a halin yanzu galibi gwamnati ba ta daukar malamai aiki, ga kuma yawancin malaman da ake ajiye aiki wanda wannan ya kara jefa yanayin aikin cikin wani hali.